Hanyoyi Guda Uku ( 3 ) Dazaka Karawa Wayarka Ta Android Saurin Browsing Batare Da Kayi Amfani Da Application Ba.
Jama,a Assalmu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci, Sannunmu Da Saduwa Daku Acikin Wani Sabon Shiri Mai Suna Koyarwa.
Acikin Wannan posting namu nayau zamu kawo muku cikakken bayani akan hanyoyi guda uku da zakabi domin karawa wayarka ta android saurin browsing.
To da farko dai abinda zakayi shine zaka shiga setting na wayarka, bayan ka shiga setting saika danna, simcards and mobile networks, idan kuma wayarka ba babba bace saika duba wurin da aka rubuta mobile data or mobile networks.
Idan kashiga wannan waje, saika danna inda aka rubuta sunan simcards din, Misali Airtel Ko MTN, Idan kuma duk mtn ne akan wayarka saika danna wanda kakeson karawa gudun browsing din.
Idan ka danna saika duba a hankali zakaga wurin da aka rubuta “prepare network type”
Idan ka danna wannan wurin zakaga kalar network din wayarka.
A wannan wuri zaka iya ganin 2G, 3G, Ko 4G.
To Anan Saika Zabi 4G Domin Yafi gudu idan kuma akan 4G din yake to shikenan saika danna back ka fito waje.
Hanya ta biyu itace idan ka duba kaga network din wayarka akan 4G Yake to saika duba kasa zakaga wurin da aka rubuta “Access Point Name” saika danna wannan wuri anan take zai kaika wurin da zaka sake karawa wayarka gudun browsing.
Kana shiga wannan wuri zakaga sunbaka damar kazabi simcard din dazaka karawa saurin browsing din, to anan saika danna kan sim din.
Daga nan zai kaika shafi na gaba saika ja zuwa kasa zakaga wurin da aka rubuta “APN Protocol” Dakuma APN Roaming Protocol.
To saika shiga ko wanne ka sanja wurin daga “IPv4″ Zuwa ” IPV4/IPV6, shikenan saikayi back ka dawo cikin setting.
Hanya ta uku kuma ta karshe itace,zaka nemi inda aka rubuta system na wayarka ko kuma wurin da aka rubuta version ram da sunan wayarka.
Idan ka shiga wannan waje saika nemi inda aka rubuta build number, idan kasami wurin saika daddanna wurin kamar sau shida zakaga yana sako wani rubutu, daga karshe zakaga yace ” yau are now a developer” to saikayi back ka koma farkon cikin setting din wayar.
Idan kaja zuwa can kasa zakaga wurin da aka rubuta system Idan Kashiga wannan wuri zakaga wurin da aka rubuta developer option, saika danna kan wannan rubutu.
Idan kaja zuwa kasa a hankali zakaga wurin da aka rubuta “mobile data always active” saika bude wannan wuri idan ba,a bude yakeba,idan kuma a bude yake saikayi back shikenan.
Dukka dukka anan muka kawo karshen wannan darasi inda muke fatan zaku danna alamar notifications domin samun sababbin shirye-shiryenmu akowane lokaci.