Muhimmiyar Sanarwa ga wanda Suka Cike aikin Npower Batch C Stream 2
Assalamu Alaikum Barkanmu da sake kasancewa daku a wannan channel namu mai Albarka HikimaTv
Ga wata muhimmiyar sanarwa ga wanda sukayi nasarar cika aikin Npower batch C stream 2
kamar de yadda kuka sani, shirin Npower: shiri ne na daukar matasa miliyan 1 wanda ya fara da daukar masu cin gajiyar 510,000 a watan Agustan 2021 a matsayin Npower Batch C stream1, A halin yanzu shirin zai sake daukar sauran masu amfana 490,000 a matsayin Npower Batch Stream II.
A yanzu haka hukumar Npower sun fitar da sanarwa akan wanda suka cika Npower Batch C stream 2
Sanarwar ita ce kamar haka: dukkan wanda yasan yayi nasarar samun sunansa a Shortlist din da aka saki na Stream 2 yayi kokari yayi thumbprint idan har bai yiba, sabo da saura lokaci kadan su rufe yin thumbprint din domin zasu fara physical Screaning nan da wasu yan kwanaki.
Dan haka duk wanda yasan yayi nasarar samu to yaje yayi thumbprint din, idan kuma Already ya riga da yayi to shikkenan baida matsala kawai sai ya tsaya ya jira mataki na gaba.
Idan kuma ka manta password dinka na Npower din ga hanya mai sauki da zaka dawo dashi: Yadda zaka dawo da password dinka na Npower
Allah ya bada sa a