Yadda Ake Maida Whatsapp Zuwa Hausa
Assalamu Alaikuma Jama’a Barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin Namu Mai Albarka HikimaTv.
Kamar de yadda kuka sani whatsapp na daya daga cikin manyan Platform wanda akafi amfani dasu a wannan lokacin Musamman wajen Chat, video call da kuma kasuwanci.
Sanin kowane Whatsapp da yaren turanci ake amfani dashi, amma a yanzu haka sun dora yaren hausa domin jin dadin masu amfani dashi, ta yadda zaka iya miyar da whatsapp dinka yazama kome da hausa.
Abun babu wuya da farko kaje Google Playstore kayi Update na Nomal whatsapp dinka, dan kuma Already kayi Update shikkenan.
Yanzu saika bude whatsapp din ka shiga menu dinsa wato wannan digon …
Daga nan saika shiga Settings
Saika shiga Chats
Sai kayi kasa zakaga inda aka Rubuta App Language saika shiga
Saika Zabi Yaren Hausa shikkenan ka gama