Tutorials

Yadda Zaka Saukar Da Kowace Irin Waka Ko Video Koda Bakasan Sunan Taba.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Jama,a assalamu alaikum barkanmu da war haka sannunmu dasake saduwa daki A cikin wani sabon post.

Acikin wannan post namu nayau zamu kawo muku cikakken bayani akan “yadda zaka saukar da kowace irin waka video ko audio koda ba,a fada maka sunan wannan waka ko video ba.

To batare da wani bata lokaci ba,bari mu kawo muku cikakken bayani.

Da farko dai dole ne yakasance ita wannan waka dakake so kana da dan guntunta a wayarka ko kuma ka iya rerata da bakinka yadda yakamata domin wani application zamu muku bayani wanda zai taimaka muku wurin saukar da wannan waka ko muce wurin taimaka muku ku gano sunan wannan waka.

Da farko idan har ka tabbatar kana da guntun wannan waka to kai tsaye saika tafi manhaja ta playstore ko google karubuta ( Shazam ) kayi download na wannam application.

Menene “Shazam” ?.

Shazam wani app ne lo Muce manhaja ce wadda take nadar sauti ko muce take sauraren sauti murya domin taimakama kasamu abinda kake bukata.

Saboda haka bayan ka dauko wannan app,saika kunna wannan guntuwar wakar,sannan ka bude datar wayarka domin baya amfani saida data.

Bayan ka bude datar saika danna wurin dakaga yana motsi wato tsakiyar wayarka,inda anan take zakaga yafara motsi wanda hakan ya nuna cewar yafara aikinsa na neman wannan waka.

Bayan yadanyi sakanni zai nemo wannan waka tare da baka sunanta dakuma sunan mawakinta,wato wanda yayi wannan waka to kaga abinda yarage ma kawai shine kaje vidmate ka rubuta sunan mawakin da sunan wakar saika saukar da ita.

Idan kuma kanaso ne ka saurari wakar kawai to zaka iya sauraronta ta cikin wannan manhaja ta shazam, domin itama kanta anyi tane domin sauraren wakoki shiyasama take taimakawa wajen dauko ko muce saukar da wakokin ta kanta.

Sai dai gudu ba hanzari ba zakuga wasu guntun wakar video ne ba audio ba kaga kuwa babu damar dazakayi ka kunna video kayi minimizing batare data daukeba, to hanya mafi sauki dazakabi shine ka maida wannan video izuwa audio.

Tayaya zan maida video zuwa audio cikin sauki ?

Amsa zaka iya maida video zuwa audio cikin sauki ta hanya biyu kachal wadda ko wace hanya mai sauki ce amma kai kana iya zaban wadda kaga tafiye maka.

Hanya ta farko itace zaka iya danne kan sunan wannan video amma saika shiga ta file manager batakan zander ko player ba,a,a takan file manager kawai,to bayan ka danne kan sunan wannan waka zasu baka option da dama irinsu move,cut,rename da dai sauransu.

To kai tsaye saika danna kan rename wato ma,ana sanja suna, ana bukatar idan ka danna wannan wuri to ka maida abin rubutunka zuwa karshe wato yar alamar nan mai kamar tsinke datake motsawa a hankali,to idan ka maidashi karshe zakaga wurin da aka rubuta .Mp4 ko .Mkv ko .3gp da dai sauransu to kaga duk wadannan abubuwar sifface dake nunama lalle wannan video ne ba wakaba.

To idan kai kuma kanaso ka maidashi waka saika goge wannan .Mp4 ko .3gp ko .Mkv dinnan saika rubuta .Mp3.

.Mp3 shine alamar da yake nuna cewa lalle wannan abu wakane ko muce audio ne,kaga kai tsaye saika kunna wannan guntuwar waka sannan ka bude datar wayanka kayi minimizing sannan kahau kan application na shazam domin saukar dashi.

Hanya ta biyu kuma itace ta hanyar amfani da mp3 converter,wadda itama zaka iya saukar da ita kai tsaye ta hanyar amfani da manhajar playstore ko kuma google search.

Domin mu saukaka muku abin batare da kunsha wahalaba ko kun bata wani lokaci ba zamu ajiye muku link din dazaku saukar da wadannan application guda biyu wato ” Shazam da Mp3 Converter.

Dafatan zaku kasance da wannan shafi namu mai suna hikimatv.ginsau.com.ng domin samun sababbin-shirye-shirywnmu akowane lokaci mungode.

Ga Link Din Daku Saukar Da ” Shazam App ” Nan.

Download Now

Ga Kuma Wanda Zaku Sauke Mp3 Converter Nan.

Download Now

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!