Tutorials

Yadda Zaka Chanja Bayananka Na BVN

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Assalamu Alaikum Warahamatullah.

Kamar yadda kuka sani ana samun wasu daga cikin mutane wanda suke da matsala ajikin bvn dinsu, kamar suna ko date of birth, ana iya samun wanda akwai gyara ajikin nasun, ga kuma yadda tsarin chanja irin wannan matsalar yake.

Karanta: Yadda Zaka Samu kyautar….

Idan kana son chanja wani bayaninka na bvn cikin sauki, to sai kabi wannan hanyar da zana kawo domin zaka chanja da kanka, ta hanyar amfani da wayarka ba tare da kaje bank ba.

Domin gyara bayanan ka na bvn, ana aika sakon bukatarka zuwa email address dinsu info@nibss-plc.com.ng tare da cikakkiyar shedar cewa wannan bvn takace: kamar bvn/nin/voter card

Yadda Zaka aika sakon domin a gyara maka shine:

Misali kanaso ka chanja number waya ne, to ga yadda zakayi:

Zakaje Gmail dinka ka shiga inda zaka aika sako saika Rubuta kamar haka:

SUBJECT: Change bvn phone number

Wajen Rubutu saika rubuta kamar haka:
Hello I lost my bvn phone number as a result of my phone being stolen, I need change my phone number.

Here is my details.

  • BVN: 2245
  • BVN Enrolled: wajen da akayima bvn
  • First Name: Sunanka
  • Last Name: Sunan mahaifinka
  • Date of Birth: Shekarar haihuwarka
  • Old phone number: Tsohuwar number ka
  • New phone number: Sabuwar number wayar da zaka chanja

Idan ka gama saika aika zuwa wannan email Address din nasu: info@nibss-plc.com.ng

Wannan shine hanyar da zaka chanja bayananka na bvn cikin sauki da kanka.

Note: amma fa ku sani, dole kome naka yazo dede da wanda yake jikin bvn, misali sunan NIN number ka yazo dede dana bvn ko voters card, Sannan kuma kaje kotu kayi affidavit na chanja number idan number zaka chanja kokuma na chanja suna, idan suna zaka chanja, saika dauki hoton sa ka hada da hotunan NIN ko voters card din, duk ka aika musu tare da message din.

Da kayi haka insha Allah cikin 24hours zasu gyara maka matsalanka, idan kuma kaga kayi kwanaki basu gyara maka ba, to ina mai baka shawarar da kaje inda akayi maka bvn din domin kayi complain.

Shiga nan domin samun wadansu bayanan👉 Shigo Nan

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!