Tutorials

Yadda Zaka Hada Layin Wayar ka Da NIN Number

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Kamar de yadda kuka sani sama da Layuka milliyon 72 aka dakatar daga Aika sako, kiran waya, sabo da basu hada sim din nasu da nin number ba.

Idan baka hada sim dinka da nin number ba har yanzu kana da saurin damar hada sim din naka da nin number, koda kuwa sun tosheka daga aika kira ko aika sako zaka iya hadawa. Matukar sunan da yake kan sim din yazo dede da sunan da yake jikin Katin Dan kasar wato Nin number.

Ga Yadda Ake hada sim da nin number:

Da farko kafin hada sim dinka da nin number dole sai kasan nin number naka, domin duba Nin number ka zaka danna
*346# a sim din da kayi katin kasa

Bayan ka danna *346# zasu nuna maka kayi Replay da 1 domin dubawa, saika danna, Nan take zasu nuna maka Nin Number ka, amma zasuyi cajin dinka wani dan kudi 20Naira

Bayan ka gano Nin number ka Yanzu sai yadda zaka Hada Layinka da nin din:

  • MTN: *785#
  • Airtel: *121*1#
  • Glo: *109#
  • 9mobile: *200*8#

Kowanne daga Cikinsu idan ka danna zasu baka zabin yadda zakabi domin ka hade Sim dinka da Nin number.

Ammafa ku sani Dole sai sunan yazo daya sunan da yake kan nin number da sunan da akayi Register sim card din dashi.

Idan kuma sunan da yake kan Sim dinka baizo daya da sunan da yake kan Nin din kaba, to koka hada bazai haduba, dan Haka Saide kaje Office din MTN mafi kusa dakai domin Suyima update na Register sim din zuwa sunan da yake kan Nin number naka.

Da fatan An fahinta.

ALLAH ya bada Sa’a ameen.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!