NYIF Sun Fara Tura Sakon Amincewa da Tallafin ₦250’000 Na NYIF Loan
Barkanku da wannan lokaci fatan kowa yana lafiya.
Wadanda suka karbi sakon da yake nuna an zabesu a tsarin NYIF, wanda aka turo sakon dauke da wasu numbobi na *5757# wanda aka bukaci daku bude account ta hanyar danna wannan lambibi *5757# kokuma ta shafinsu na Internet kokuma ta branch mafi kusa dakai.
A yanzu haka de wadanda suka karbi wancan sakon, anan ci gaba da amincewa da basu Rancen na kimanin Naira ₦250’000.
Dan Haka ana sanar da duk wanda yasan ya ga wancan sakon mai dauke da *5757# ta message kokuma ta email, da yayi kokari ya duba Email Address dinsa, Cikin Folder Spam Folder Zaiga Sakon amincewa da Bashi ranchen ₦250’000 Bayan ganin sakon Ana bukatar da kayi Accept na loan offer, Wanda yake dauke da sakon da suka turo maka ta Spam folder.
Dan haka duk wanda yasan sun tura masa wancan sakon, ko basu tura masaba, to yayi kokari yaje ya duba email dinsa Cikin Spam folder. sabo da bayan Accept na loan offer, daga nan sai batun fara turo kudin.
Sannan duk wanda ya samu wancan sakon yayi kokari ya bude account din kamar yadda suka bukata.
Allah ya Taimaka Allah ya bada Sa’a