Muhimmiyar Sanarwa Daga Hukumar Npower
Assalamu Alaikum Warahamatullah.
A jiya ne 14/6/2022 Ofishin Npower suka fitar da sabuwar sanarwa kan cewa a Physical Verification din da za’a fara 14th June 2022 na rukunin Npower Batch C
stream II
Za’a tantance iya wa yanda suke yan Npower Graduate, su kuma wa yanda suke Non-Graduate za’a tantance su daga baya a wurarin da za’ayi musu training na koyon sana’o’i.
Banbacin Graduate da kuma Non-Graduate:
Graduate: sune wa yanda suka cike tallafin Npower da takardun makaranta na gaba da sakandare (Degree, NCE, HND, ND & OND).
Non-Graduate: Sune wa yanda sunka cike tallafin Npower da takardun makarantar da basu wuce sakandare ba ko kuma ma basuda takardun makaranta gabaki ɗaya (SSCE & None)
Sukuma masu takardun secondary dama wanda basu da takardun zasuyi nasu ne a can inda aka turasu domin a koya musu sana’a.
Allah ya bada sa’a