Yadda Zaka Cika sabon shirin MTN Pulse ‘Blow My Hustle
Kamar yadda kuka sani wannan wani sabon shiri ne da kamfanin mtn suka shirya domin tallafawa yan nigeria ta hanyar basu horo da kuma tallafi
Mutane 20 za su yi tafiya da tsabar kudi da horon da ya kai Naira miliyan 68 (N68,000,000) don kai wa ga mataki na gaba, yayin da tallafin kasuwanci, horo, da bayanai ke samuwa ga duk wanda ya kai matakin karshe.
Kamfanin MTN Pulse mai suna ‘Blow My Hustle’ an hada shi ne domin nuna hazakar matasan ‘yan kasuwa masu kwarin gwiwa a Najeriya tare da ba su karfin gwiwa ta hanyar nishadi da nishadi.
Danna Apply here dake kasa don yin Register
Bayan ka shiga ya bude saika shigar da bayananka sannan ka zabi bangaren da kakeso, sai kuma kayi bayanin dabai wuce kalmomi 200 ba game da dalilinka na shiga shirin
Sannan saika dora videon na kamar second 90 domin masu dubawa su yi hukunci akan shirin naka.
Allah ya bada Sa’a
Lokacin rufewa: October 30, 2022