Uncategorized

Tambayoyi 7 da mai amfani da
Wayar Android ya kamata ya san amsarsu

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Android wacce ake furta ta da Hausa anduroyid
manhaja (OS) ce da kamfanin Google Media Inc
da ke kasar Amurka ya mallaki lasisinsa wanda
shi wannan manhajar ake amfani da ita a kan
wayoyin hannu da kuma ƙananan kwamfutocin
hannu da ake kira da Table PC.
Su irin wannan wayoyi na Android ba kamar
sauran waya ba ce kasancewar ita tsarin riƙe ta
da tsarin amfani da ita ba a ko’ina ake yi ba.
Shi ya sa na ga ya dace in yi mana bayanai a
kan waɗansu tambayoyi guda bakwai da ya
kamata mai amfani da waɗannan wayoyi ya
sani kuma ya san yadda zai amfani da ita.

1) Dole ne sai na yi amfani da Google Accout
kafin in iya amfani da Android?
Haka yake! Dole duk wanda ya sayi waya ko
kuma tablet ya zama yana da account tare da
kamfanin google kafin ya yi amfani da ita.
Amma wannan ba yakebance cewa akwai wani
ɓangare na google accout wanda ya zama
wajibi ne a ce shi ne mutum zai yi amfani da
shi ba. Abin da ake so kawai ka yi rajista da
kamfanin ta wurin mallakar ɗaya daga cikin
abubuwan da suke gabatarwa na ayyukansu,
kamar gmail da makamantansu. Kodayake
google yana ba mutum damar kara wani imel
wanda ba google ba, sai dai duk lokacin da
mutum yake son ya shiga ya ƙara wa wayar
tashi ko tablet dinshi kuzari ko kuma ya kara
mata wani application, to dole sai in yana da
account tare da google. Kuma akwai waɗansu
abubuwa masu matukar amfani ga mai amfani
da wayar android ko tablet wanda idan mutum
ba ya amfani da account na google ba ne, to
ba zai same su ba.

2) Wace hanya ce ta fi kyau wacce zan bi in
kwashe duk sunayen da suke cikin wayata?
Akwai hanyoyin da mutum zai iya bi domin ya
ga ya kwafe tsofaffin lambobin cikin wayarsa
zuwa wayarsa ta android. Ɗaya daga cikin
hanyar shi ne mutum zai iya buɗe google sai ya
shiga dakin aikawa da sakon imel wanda ake
kira da gmail, to sai ya rubuce dukkanin
sunayen da ke wayarsa daga nan lambobin da
kansu za su dawo cikin wayarsa ko kuma
tablet pc ɗin shi. Ko kuma ka yi amfani da
tsohuwar hanya na kwafe lambobinka a cikin
SIM ɗinka sannan ka saka shi cikin wayar
android ko tablet sannan ka kwafe shi cikin ta.

3) Mene ne dalilin da ya sa wayoyin android ba
sa kama da juna?
Kamfanin google su suka kirkiri manhajan
Android amma kuma sai suka bai wa
kamfanonin da suke yin waya damar su yi
amfani da wannan manhajar a cikin wayoyinsu.
Saboda haka shi ya sa kake ganin fuskokin da
kuma kamanninsu ya banbanta. Kamfanonin
da suke da wannan lasisi sun haɗa da
kamfanin Samsung da kuma kamfanin HTC,
wanda waɗannan kamfanonin kowannensu,
kera waya da kuma kayan Kwamfuta yake yi.
Saboda haka kowane ɗaya daga cikinsu yana
da damar ya yi irin kalar waya ko kuma tablet
da yake ganin za ta amsu a hannun abokanen
cinikinsa.

4) To yaya za a yi in samu android wacce ba ta
waɗancan kamfanonin ba?
Idan baka son ɗaya daga cikin wayoyin da
kamfanin HTC ko Samsung suke yi, to ai
kamfanin google yana da tashi wayar mai suna
NEXUS. Wanda aka fi sani da Nexus 7 Tablet
da kuma Galaxy Nexus Phone. Waɗannan
guda biyu da manhajar da kuma karafan da
suke jikinsu duk mallakar kamfanin google ne.
Sannan kuma su waɗannan wayoyi ko da wane
lokaci kamfanin google yana ƙoƙarin inganta su
ta wajen manhajin da suke amfani da su,
kasancewar suna samun komai kai tsaye daga
wurin google. Su kuwa sauran wayoyi kamar
na HTC da Samsung waɗanda suke amfani da
manhajar android sukan ɗauko wani lokaci mai
tsawo kafin a waiwayi manhajar tasu, domin
abu ne mai yawa da kuma faɗi da kuma
abubuwan da waɗancan kamfanonin suke yi
yana musu yawa.

5) Mene ne banbanci tsakanin Home Screen da
kuma App Drawer?
Shi App Drawer shi ne wurin da za ka samu
dukkanin application da ka ɗaura wa android,
an kira wurin da Drawer kamar yadda malam
Bahaushe ya sani da matsayin rumbu
kasancewar nan ne ake samun abubuwan da
aka ajiye a ciki. Saboda haka Adroid suna da
fallaye guda bakwai da suka baka damar ka
fito da dukkanin application da kake yawan aiki
da su, domin samun sauƙi. To, waɗannan
application da ka saka a kan wannan falle shi
ake kira da Home Screen . Su kuma application
da baka son ganinsu a wannan fallen su kuma
suna cikin App Drawer.

6) Mene ne Widgets?
Widget kamar yadda ake furta su da Hauwa
“wijet” suna da amfani matuka domin su ana
amfani da su wajen bayar da waɗan su
bayanai da kuma tattalin wutar batirin android.
Su kamar hotuna ne na waɗansu application
da ka saka a cikin Home Screen ɗin ka wanda
za su riƙa faɗa maka abubuwan da yake
gudana ƙarƙashin waɗannan application da ka
saka su a cikin wijet ɗin. Misali wanda ya
ɗauko application na facebook ko twitter ko na
gmail ya saka a cikin wijet to duk sakon da ya
shigo, ɗaya daga cikin waɗannan application
ɗin zai ga matashiya kai tsaye wanda ba sai ya
buɗe shi application karan kansa ba.

7) Ina da abubuwan saurare a itunes zan iya
sauraronsu a android dina?
Akwai wani software da ake kira da
doubleTwist yana aiki kamar yadda ka san
Itunes yake yi. Saboda haka idan ka ɗaura shi
zai baka damar saukar da duk abin da kake da
su a Itunes zuwa Android ɗinka.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!