Sanarwa Ta Musamman Zuwa Ga Duk Wanda Yake Amfani Da Bank Account
Assalamu Alaikum jama’a barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.
A yau nazo muku da wata sanarwa ta musamman ga duk wanda yake amfani da banki.
Kafin Mu Kawo Muku Wannan Sanarwa Ko Bayani Wanda Ko Wane Banki Ya Dade Yana Bayani Akansa Zamuso Ku Danna Alamar Allow Da Kuke Yawan Ganin tana Baiyana A Cikin Wayoyinku A Duk Lokacin Da Kuka Ziyarci Wannan Shafi Namu.
To A Wannan Sanarwa Da Zamu Kawo Muku Zamuyiwa Wasu Tuni Daga Cikin Wadanda Sukasan Wannan Matsala Da Take Faruwa Ga Dukkan Wani Ko Wata Wadda Ta Bude Account Na Banki.
Wannan Matsala Ta Dade Tana Damun Mutane Wanda Hakan Yana Faruwane Saboda Rashin Sani Dakuma Karancin Ilimin Boko Daya Faruwa A Wannan Zamani.
Idan Mukace Karancin Ilimin Boko Bawai Muna Nufin Mutum Baya Karatun Boko Ko Baitaba Yiba, A,a Zata Iyu Kana Karatun Amma Kuma Saiya Kasance Baka Iya Karantawa Sannan Baka Iya Fahimtar Abinda Aka Fadamaka Ko Aka Rubuta Maka.
To Kaga Kuwa Su Banki Suna Amfani Ne Da Yaren Turanci Wanda Idan Baka Iya Karatu Da Rubutu Dakuma Sanin Fassarar Turancin Yadda Yakamata Ba, To Bazaka Taba Gane Bayanin Da Sukeyiwa Customers Dinsu Ba.
To Wannan Dalili Yasa Mukace Bari Muyiwa Mutane Bayani Akan Irin Bayanan Da Banki Sukewa Duk Wani Wanda Yabude Sabon Account Kai Harma Da Wanda Suka Dade Da Budewa.
Har Gobe Banki Duk Lokacin Da Ka Tura Kudi Ko Aka Turoma To Sunawa Mutane Gargadin Cewar Kadda Ka Yadda Wani Ko Wata Ko Wasu Su Tambayeka Wani Abu Wanda Ya Danganci Bankinka Kai Kuma Ka Fada Musu.
Saboda Ansha Sacewa Mutane Kudadensu Sau Da Yawa Batare Da Sanin Bankinba, Dalili Anan Su Wadannan Barayi Idan Suka Duba Sukaga Kana Ajiye Kudi Ko Ka Bude Sabon Account To Hankalinsu Zai Dawo Kanka.
Zasuyi Iya Kokarinsu Ta Hanyar Yan Dabarun Da Suke Dasu Domin Tambayarka Cewar A Cikin Account Dinka Akwai Matsala Saboda Haka Kabasu Wasu Numbers Ko Wata Number Daga Jikin Atm Card Dinka Domin A Gyarama Wannan Matsala.
To Abinda Sukuma Banki Suke Gargadi Kenan Har Gobe Cewar Su Bazasu Taba Kiranka A Waya Ko A Wani Abu Su Tambayi Wasu Numbobi Dake Jikin Card Dinka Ko Su Tambayi Numbers Wanda ZA,a Turo Daga Kan Layinka Ba.
Suna Gargadin Cewar Duk Sanda wani Ya Kiraka Yace Ka Bashi Wasu Numbers Ko Wata Number Ko Number Ta Sirri Wadda Kake Cirar Kudi To Kadda Ka Bada.
Idanma Abin Ya Shige Maka Duhu To Kaje Wannan Banki Daka Bude Account Kamusu Korafi Akan Abinda Yake Faruwa, Kuma Suma Idan Kaje Ka Musu Bayanin Abinda Dai Zasu Fadama Bai Wuce Abinda Na Fadama Yanzu Ba.
Inda Muke Fatan Wannan Sanarwa Dakuma Tunatarwa Zata Amfani Mutanen Da Basu San Wannan Matsala Datake Faruwa Ba, Wanda Har Yanzu Ana Sacewa Mutanen Da Basu San Wannan Abuba Kudadensu.