Dama ta samu: Yadda Zaku Shiga Gasar Samun Kyutar ₦650,000 zuwa sama
Assalu alaikuma warahamatullah barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka na hikimatv.
Ga wata sabuwar dama ga matasa, wato yadda zaku shiga gasar samun kyautar naira 650,000 zuwa sama da haka ta Cyber security
Ma’aikatar Matasa da Cigaban Wasanni ta Tarayya ta ƙaddamar da shirin Cyber Security, horo, Gasa, Takaddun shaida, horarwa da samar da ayyukan yi ga matasan Najeriya. Wannan shiri ne na
ma’aikatar tare da haɗin gwiwar Halogen Group wanda aka tsara don cin gajiyar matasa. An yi wannan horon ne don jan hankalin matasa akan damar Cyber Security don ba da damar rage haɗarin
hare-haren ta hanyar Intanet, tare da bayarda takaddun shaidar horo ta Cyber Security wanda zai iya ba da damar samun aiki a cikin gida da waje ga mahalarta.
Sannan kuma akwai kyaututtukan N1m, N650,000, N350 000 ga wadanda suka lashe wannan gasar ta Cyber security.
Domin shiga wannan gasa danna link din da yake kasa
Shigo nan don cikawa
Allah ya taimaka