Nirsal Sun Sake Bude Shafinsu Domin Bada Tallafin kudi Naira 500,000
Assalamu alaikuma barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yananan cikin koshin lafiya.
Idan baku mantaba abaya na kawo muku wannan tallafin na nirsal kuma na koyar da yadda zaku cika, kuma Alhamdulillah mutane dayawa sun cika wasu daga ciki sun samu.
A yanzu haka Bankin Nirsal Microfinance ya sake buɗe shafin nasa domin neman rancen marar kudin ruwa wato non Interest loan.
Hukumar NMFB ta lura cewa waɗanda za su ci gajiyar shirin a cikin sabon rance mara ruwa NIB COVID-19 yanzu za su iya zaɓar wanda yayi musu da kansu akan ingantacciyar hanyar samun rance ta NIB COVID-19 dangane da wuraren da aka fi so
Hukumar NMFB tun da farko a cikin wata sanarwa ta fayyace cewa tsarin rance na COVID-19 na NIB na duk ‘yan Najeriya ne ba tare da la’akari da ra’ayin addini ba. Wato, rancen COVID-19 na NIB ba a nufin Musulmai ne kawai ba.
Abubuwan da ake bukata wajen Neman Wannan tallafin:
- Dole ne ya cika shekaru 18 zuwa sama,
- Dole ne ya kasance yana da BVN
- Dole ne ya kasance yana gudanar da kasuwanci
Domin Neman wannan Rancen Saiku shiga Link din dake kasa
Shigo nan don Cikawa
Allah ya bada sa’a