Dalilin Da Yasa Har Yanzu Ba’a Turawa Wasu Tallafin 30’000 Na RRR Ba
Jama’a Assalamu Alaikum Barkanmu da wannan lokaci da fatan kun tuna Lafiya.
Kamar de Yadda kuka Sani wannan Tallafin Na RRR wato (Rapid Response Register) tallafi ne da gwamnatin Tarayya ta fito dashi domin bada tallafin Naira 5000 na tsawon wata shiga ga Talakawa, wanda daga baya aka hadeshi ya zama 30’000.
Shide wannan tallafi na RRR tallafine da gwamnati ta fito da wasu numbobi wanda ake dannawa a matsayin code din da zakayi Register, wanda bayan kayi Register daga baya za azo a kafe sunaye a unguwanni daga baya sai kuma azo a karbi bayananka kokuma a kiraka a waya kaje kakai bayanan naka.
Bayanan da suke karba sune kamar haka:
- Full Name
- Date of bith
- BVN
- Acc number
- NIN Number
- Shekara
- Sunan kaka
- Da sauransu
Bayan an karbi wannan bayanan daga baya sai kuma a turo maka da kudinka kimanin naira 30’000, wadanda suka cike a mataki na farko tuni de suka jima da karbar naira 30’000 din nasu.
Dalilin da yasa wasu kuma har yanzu ba’a turo musu 30’000 din nasu ba.
Mutane dayawa sun cike wannan tallafin na RRR saide kuma har yanzu basu karbi kudin nasuba, dalilin rashin samun kudin kuwa shine, kode sun bayar da bayanai ba dede ba kokuma an samu matsala wajen shigar da bayanan nasu.
Dan haka idan har ka cika kuma ba,a karbi bayanan kaba to gaskiya baza ka samu kudin nakaba domin dole sai an karbi bayananka sannan za a turo maka kudin naka.
Wasu kuma sunyi amfani da code na RRR wanda bana jihar suba bana garin suba, dan haka bai zama lalle idan an kafe sunayen wanda suka cikaba kaga sunanka sabi da baka garin, duk dama wasu suna iya kira ta waya, amma akwai mutanr dayawa wanda sun cika na wani jihar sakamakon basu samu na jihar suba da wuri.
Wasu kuma sun cika amma bayanansu da suka bayar baiyi active ba, dan haka anabi unguwa unguwa ana sake karban bayanai, dan haka idan anzo unguwarku da niyyar sake karban bayanai inde an kafe da sunanka to kayi kokari ka sake bayar da bayananka domin wanda ka bayar da farko bai yiba.
Wannan de shine dalilin da yasa ba a biya wasu kudin RRR ba.
Dan haka karka damu idan har kasan ka bayar da bayananka daidai to ka kwantar da hankalinka insha Allah zaka samu kudinka very soon
Allah ya taimaka ameen