Sanarwa ga Wanda Suka Cike Tallafin Kudi Na NYIF
Assalamu alaikum jama’a Barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka HikimaTv
Kamar de yadda kuka sani shirin NYIF wato Nigerian Youth Investiment Fund, Shiri ne da gwamnati ta shiryashi domin bayar da tallafin bashi ga matasan Nigeria domin su dogara da kansu.
Wannan shiri de shiri da aka jima da yinsa wanda tuni wasu daga cikin wanda suka fara cikawa tuni suka faracin gajiyar shirin.
Idan baku mantaba a kwanannan NYIF suka amince da Rancen wasu daga cikin wanda sukayi training wanda tuni de wasu daga ciki suka karbi kudinsu, wasu kuma har yanzu basu karba ba duk da sunyi training.
Sannan kuma NYIF sun fitar da wasu bankuna wanda suka bada damar duk wanda aka amince dashi, ya bude acc a karkashin wannan bankin domin anan ne za a turo masa kudinsa, wasu daga ciki sun bude wasu kuma basu bude ba,
Dan haka sanarwar itace kamar haka:
Duk wanda suka bude ba a turo musu kudinba, to su kara hakuri domin bankunan suna bada hakuri kan rashin turowa, musamman Bankin Lapo Microfinance bank yana neman afuwa ga wanda zasu ci gajiyar shirin asusu saka jarin matasan najeriya NYIF musamman masu asusun ajiya na bankin game da sakin rancen NYIF. Suna aiki domin magance duk ƙalubalen da zaa fuskanta wajen sakin kudin ga masu cin gajiyar shirin cikin sa’o’i 36 masu zuwa zaa saki
kudaden izuwa asusun ku.
Allah ya bada sa a