Loan & Support

Sanarwa ga Wanda Suka Cike Tallafin Kudi Na Nirsal Non Interest Loan

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Assalamu Alaikum Barkanmu da wannan lokaci da fatan kuna cikin koshin Lafiya.

Kamar de yadda kuka sani Nirsal Non interest loan, wani tallafi ne na bashi marar kudin Ruwa wanda gwamnatin tarayya ta fito dashi ta hannun bankin nirsal domin a taimakawa talakawa da masu kananan karfi da bashi na kimanin naira 500’000 zuwa sama.

Idan baku mantaba wannan tallafi na nirsal tallafine da aka jima da yinsa wanda tuni wasu daga cikin wanda suka nema a farko farko aka fara biyansu, duk dama shi wannan tallafi na non interest loan, kaya za a bayar ba kudi ba, shiyasa a wajen neman suka bada damar ka sanya kayayyakin da kakeso wanda shine za a baka na kimanin naira 500’000 amma duk da hakan wasu vendors din suna bada kudi a madadij kayan.

Karanta: Yadda zaka Cike Sabon program na hukumar NiTDA

To sanarwar itace a yanzu haka wannan tallafi na Nirsal Non Interest Loan sunaci gaba da tura sakon Accept offer later, wanda wannan sakon shi yake nuna an amince da rancen daka nema shiyasa aka baka damar ka amince da yarjajjeniyarsu, dan haka suna turo sakon ta message sabo da haka sai a duba da zarar kaga sakon saikabi link din da suka nuna maka domin accept na offer later din.

Sannan Kuma ku sani ada suna accept na 500’000 amma yanzu haka sun Rageshi dan haka koda abaya sun amince da rancen 500’000 a gareka, inde har yanzu basu turo maka kudin kaba, to idan sun tashi turowar zasu turo maka 300’000 dan haka kada ku damu idan kunje wajen accept na offer latter kunga kudin da aka amince muku ya koma 300k

Dan haka anaci gaba da tura sakon sai ku zauna cikin shiri insha Allah inde da rabo zasu turo maka.

Allah yasa mu dace

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!