Muhimmiyar Sanarwa Ga Wanda Suka Cike Tallafin Kudi Na P-YES
Assalamu Alaikum Warahamatullah, Barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka Hikimatv.
Kamar de yadda kuka sani Shirin P-YES wani shiri ne da aka shirya domin Karfafawa Matasa gwiwa, wanda Shugaban Kasa ya kirkiro, Sannan an
tsara shi ne don gudanar da hadin gwiwa da gwamnatocin Jihohi, kungiyoyi masu zaman kansu don samar da wani tsari na saukaka ayyukan yi ga matasa a Najeriya.
Karanta: Yadda Zaka Cike tallafin kudi na…
Manufarmu Wannan shirin ita ce karfafa matasan Najeriya ta hanyar samar da
damammaki da kuma samar da yanayi na samar da arziki ta hanyar baiwa matasa sana’o’in hannu, ilimi da albarkatun da za su sa suyi amfani, ta yadda za a rage radadin talauci da samar da dimbin matasa masu karfin tattalin arziki wadanda suke da dabarun da za su iya amfani da su. ta hanyar kirkire-kirkire da ma’ana suna ba da gudummawa ga gina kasa.
A Yanzu haka ana cigaba da bawa wadanda suka nemi shirin P-YES tun
2019 damar Kirkirar Password dinsu ta hanyar tura musu sako ta Email dinsu
Dan Haka idan kana cikin Ka hanzarta ka duba Email dinka Wato Spam Folder
domin saita password.
Allah ya bada Sa’a