Loan & Support

Dalilin Dayasa Har Yanzu Ba a biya Wasu Tallafin Kudi Na Survival Fund Ba

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Jama’a Assalamu Alaikum Barkanmu da wannan Lokaci da fatan Anyi Sallah Lafiya Allah ubangiji ya maimaita mana ameen.

Kamar de yadda kuka sani Survival Fund Wani shiri ne da gwamnatu ta shirya domin bayar da tallafi ga talakawa ta hanyar basu kudade kimanin naira dubu 90k wasu kuma 120k.

Wannan tallafi de mutane dayawa sun samu damar samun wannan kudi, amma kuma duk da hakan akwai wadanda sun cika tun dadewa kuma anyi verified nasu amma har yanzu ba a turo musu kudin suba.

Dan haka ga dalilin da yasa ba a turowa wasu kudin suba:

Dalili Na Farko shine: Bada Incorrect Details Na Ma,aikatan Kamfaninka, muddin kasamu matsala irin wannan to survival fund suna iya kin karban kamfaninka, barantana suma verify,

Mafiya Yawan Mutanen Da Suke Bude Kamfani Suna Samun Matsala Wajen Cike Bayanan Da Ake Bukata Kamar Yadda Yakamata, indai bayananka Basu Cika Dai Dai Ba, Ko kuma sukayi tsammanin Akwai Son Zuciya A cikin Bayanan Da Ka Cike To Zaiyi Wahala Su Karbi Kamfaninka, Barantana Kuma Suma Verify,

Dan haka duk lolacin da zaka cike wannan tallafi wanda ya danganci gomnati, ka tabbatar ka shigar da kome daidai sabi da gudun matsala.

Bayan Wannan Tallafi Akwai Sauran Tallafi Da Dama Da Nigeria Ta Fitar Domin Tallafawa Yan Kasar.

Saboda Haka Saiku Kasance Da Wannan Site Namu Domin Samun Hanyoyin Dazaku Cike Irin Wadannan Abubuwa.

Domin Karin bayani: Tallafin Kudi Daga Survival Fund

Allah ya bada sa a

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!