An Fara Cire Slip Na Jarabawar Jamb 2022
Assalamu Alaikum Jama’a Barkanmu da wannan lokaci da fatan kuna lafiya
An fara cire Slip na Jarabawar JAMB na wannan shekarar a inda dalibi zai zana, Lokaci da wurin da zai zana wannan jarrabawa kamar haka.
A yau ne hukumar ta bada damar fara cire wannan slip domin dukkan daliban da sukayi rejistar su iya ganin rana, lokaci da wurin da zasu zauna wannan jarrabawa a duka fadin kasarnan.
Wannan bayanai ya nuna cewa abun yazo inji mai tsoron wanka! Dan haka dukkan dalibai sai su kara zage dantse kuma su kara kaimi domin tunkarar jarabbawar ta bana domin kuwa hukumar ta tsayar da ranada lokaci domin komai ya tafi kamar yadda ta tsara.
Sannan a wani bangaren daban kuma an gargadi dalibai mata da su guji amfani da kunshi mai a lokacin jarrabawar domin kuwa yatsu basu cika daukar na’urar thumb print ba kuma duk wace batayishi ba ba zata zauna jarrabawar ba.
Zaku iya cire exam slip dinku na jamb ta wannan hanya Jamb – Print Examination Slip ko kuma zaku iya zuwa Internet Cafe mafi kusa da ku domin a duba muku.
Source: HausaDrop