News

Hukumar JAMB Ta Sanar da Ranar Rufe Yin Rijistar Jarrabawar UTME/DE 2022

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Hukumar shirya Jarrabawar shiga Makarantun gaba da Sakandare, JAMB ta jaddada matakin rufe yin rijistar jarrabawara ranar Asabar, 26 ga watan Maris.Hukumar ta sanar da haka ne a yau Litinin a Abuja a mujallar mako-mako da ofishin Babban Rijistara ke fitar wa. A cewar JAMB, a ranar 26 ga Maris ɗin za ta rufe sayar da katin yanar gizo na rijistar Haɗaɗɗiyar Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandare, UTME da kuma nashiga Makarantun Gaba da Sakandare kai Tsaye, DE.”Mun ɗauki wannan matakin ne sabo da yadda mu ke ganin yadda ake sayar da katinan yanar gizo ke ƙaruwa amma kuma ɗaliban da kezuwa cibiyoyin jarrabawar na raguwa.”Za a iya tuna cewa hukumar JAMB ta ce ba za ta tsawaita wa’adinyin rijistar da hukumomin da su ke saman ta su ka bata ba.”Sabo da haka duk wadanda su ke da sha’awar yin rijistar su
hanyarta su je su yi kafin ranar rufewar,” in ji mujallar.Hukumar ta ce a halin yanzu ɗalibai 1, 512, 739 su ka yi rijista da garanar 29 ga Maris.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!