NYIF Sun Fara Approve Na Kudaden Da Aka Nema
Assalamu alaikum Warahamatullah.
Kamar de yadda kuka sani wannan wani shirine da gwomnati ta shirya shi tun a shekarar 2021 wanda ake kira Nigeria Youth Investment fund (NYIF) kuma shiri ne da aka shirya domin tallafawa matasa da masu kananan karfi ta hanyar basu bashin kudi kimanin 500’000 wanda tun a wancan lokacin aka fara bawa wasu daga cikin wanda suka nema kuma sula gabatar da training.
Bayan wasu lokaci anci gaba da biyan wanda suka nema yayin da aka sake bada sabuwar dama ga wanda basu nemaba domin suma su nema aci gajiyar shirin dasu.
Akwanan baya kuma an fitar da list na mutane 10’000 wanda sukayi nasarar shiga cikin shirin, yayin da aka turawa wasu daga cikin mutun 10’000 sakon training kuma suka gabatar da training din.
Bayan haka kuma a kwanannan anci gaba da turawa wanda sukayi training din dama wanda basuyiba, sakon bude sabon account a bankin NPF Microfinance Bank.
Kuma suna yiwa mutane approve na kimanin 800,000 wasu 700,000 wasu 500,000 wasu 300,000 wasu 250,000 wasu 200,000 da sauran su.
A yanzu haka de wanda suka karbi sakon bude account A na sake tura musu wani sako wanda yake dauke da Offer letter wacce zasuyi download su cike sannan su miyar musu ita.
Yadda abun yake shine: idan ka samu sakon offer latter, idan kuma baka samuba zaka iya duba email dinka musamman cikin spam folder, idan har sun turo maka zaka ganta, abin da zakayi shine zakayi download dinta, sannan sai kayi printing dinka, ka cike duk abubuwan da ake bukata, daga nan sai ka dauketa a hoto kokuma kaje ayi maka scanning dinta bayan ka gama cikewar sai ka miyar musu ta hanyar yi musu replay da ita ta email din da suka aiko maka wannan sakon.
Idan kuma ka kasa download na offer Letter saika danna wannan link din domin yin download dinta kai tsaye
Note: amma ka sani dole saika karbi wannan sakon sannan zakayi amfani link din domin cike offer letter.
Kuma kamar de yadda NYIF din suka fada wannan shine mataki na karshe daga shi saide ku jira shigowar kudinku zuwa cikin asusun bankin ku.
Wadanda kuma ba’a turo musu sako na training ko na bude account, su kwantar da hankalinsu, kuma suci gaba da duba email dinsu musamman cikin spam folder, suci gaba da dubawa a koda yaushe domin zasu iya samun sakon a kowane lokaci.
Allah ya bada Sa’a