Yadda Zaka Samu Tallafi Na Horo A Bangaren Noma Daga Kungiyar Youth In Agrifood
Assalamu Alaikum Warahamatullah, Barkanmu da Sake kasancewa Daku a wannan shafin Namu Mai Albarka Na Hikimatv
A yau nazo muku da wata hanya da zaku samu horo a bangaren noma daga wata kungiya mai suna Youth Agrifood Export Development, wanda zasu bada Horo na Tsawon Watanni Shida.
Shi de Wannan Shirin Na Agri-Food Export Development Programme(YAEDP) shiri ne na watanni shida da aka tsara don haɓaka ƙarfin matasan Najeriya 5,000, masu shekaru 25 – 40 don shiga harkar fitar da kayayyaki zuwa ketare. Shirin zai ba da horo, haɗin kai na kasuwa, da tallafin dijital ga ƴan kasuwa da shugabannin haɗin gwiwa a fannin noma a Najeriya.
Abubuwan da Ake bukata Wajen Cike Wannan Program:
- Dole ne mai nema ya sami kasuwancin aiki na akalla shekara guda
- Dole ne ya zama yana da shekaru 25 zuwa 40
- Dole ne ya zama manoni ko mai siyarwa
- Dole ne mai nema ya kasance daga lissafin jihar da ke ƙasa
- Abiya
- Adamawa
- Cross River
- Edo
- FCT
- Kano
- Kaduna
- Kogi
- Legas
- Ogun
- Oyo
Domin Shiga Cikin Wannan Shirin Ka danna Apply da yake kasa
Apply here
Bayan ka danna Apply here zai kaika shafin, sai kayi kasa kadan zakaga Inda aka Rubuta BEGIN saika danna wajen anan zai kaika inda zaka shigar da bayananka.
Allah ya bada Sa’a
Za’a Rufe a Ranar: April 30th, 2022