Yadda Zakayi Register Na NEDC Domin Samun Horo da Tallafi da kuma Jari
Kamar de yadda kuka sani wannan shiri za a bayar da horo ne tare da bada kayan aiki da kuma jari, kamar yadda wannan kungiya ta NEDC suka saba duk shekara.
Abubuwan da Za,a bayar da horon akansu sune kamar haka:
- Graphics Design
- Smartphone Repair
- Stellite Terminal Instalations
Wannan sune abubuwan da Za a bayar da horo akansu, Sannan Za,a bayar da horon ne wati training na tsawon Wata biyu a kowace Center na training daka zaba a yayin Yin Register.
Sannan Za a bayar da horon na tsawon awa biyu a kowace Rana daga Litinin zuwa Lahdi.
Domin yin Register saika Shiga Apply dake kasa
Apply here
Bayan ya bude zai kawoka shafin da zakayi Register, wato zaka shigar da bayananka da kuma garinka da jiharka, sannan saika zabi inda zakayi Training da kuma irin abun da kakeso a baka horo akai, kamar koyan graphics, ko gyaran waya, kokuma gyaran stellite.
Bayan ka kammala cikewa saika danna inda aka Rubuta Register shikkenan ka gama Register.
Daga nan Zasu tura maka da sako ta email dinka wanda yake dauke da Username da Password dinka, da kuma karin bayani akan shirin, daga nan sai kayi copy na username da password kazo kayi login ka shiga Dashbord dinka.
Shikkenan ka gama saika jira ranar da zaka fara taraining.
Allah ya bada sa’a