Yadda Zaka Gane Ko Kana Cikin Masu Cin Gajiyar Tallafin ₦30’000 Na RRR
Assalamu Alaikum Warahamatullah, Barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka Na hikimatv
Kamar de yadda kuka sani shi wannan tallafi na RRR wato Rapid
Response Register: shiri ne da gomnatin Nigeria ta shirya domin tallafawa talaka da kuma marasa karfi, tare da wanda Annobar korona ta shafa.
Kuma wannan tallafi an shirya shine akan za a bada Naira 5000 har tsawon wata shida, wanda aka gabatar shiga cikin shirin ta hanyar danna wasu lambobi, daga bisani bayan an gama shiga ta hanyar danna lambobi sai aka kafe sunayen wadanda suka Cike a kowace unguwa, sannan akazo aka karbi bayanansu domin shigar dasu cikin tsarin.
Yadda zaka gane ko kana cikin wannan tsarin na RRR
Bayan ka tabbatar da kayi Register tsarin ta hanyar danna wasu lambobi, daga nan bayan wani lokaci, anabi kowace unguwa ana kafe sunan mutane wanda suka shiga tsarin, sannan kuma daga baya akazo ake karban bayanai kokuma a kiraka a waya a karbi bayananka kamar haka:
- Full name
- BVN
- Account Number
- Account Name
- Bank Name
- NiN number(optional)
- Daukanka a photo
Wadannan Abubuwa sune ake karba bayan an gama register, ko azo har gida a karba kokuma a kiraka a waya ka tura.
Idan har ka cika kuma ka bayar da bayananka to karka damu za’a tura maka kudinka Naira 30’000, nasan wasu zasuyi mamakin tura 30’000 da akeyi a maimakon 5000 da akace Za’ana turawa duk wata wata.
Dan haka inde kasan ka bayar da bayananka to karka damu insha Allah Zaka samu sakon 30’000
Idan kuma baka cikaba saika shiga nan nan domin duba na jiharka:
Yadda Zaka Cike Tallafin kudi na RRR
Allah ya bada Sa’a