Yadda Zaka Duba ShortList na Nexit Loan
Assalamu alaikum, barkanmu da wannan lokaci sannunmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka hikimatv.
A yau nazo muku da shortlist na Next loan.
Kamar de yadda kuka sani Nexit Load wani shiri ne da Gwamnati ta shirya domin bada Rance ga wadanda sukayi aikin Npower na Bach A da B, wanda aka shirya basu lamunin bashi daga Naira 500k zuwa sama, ga wadanda aka horas dasu.
Idan baku mantaba Sadiya umar faruq ta sanar a shafinta na Twitter cewa za a fara horas da rance na kwanaki 5 na NEXIT daga ranar 14 ga Maris zuwa 18 ga Maris, 2022. Da take sanar da fara horas da rancen NEXIT, Misis Anibueze ta bayyana cewa daga cikin wadanda suka ci gajiyar Npower 500,000 mutun 370’000 suka ci gajiyar Npower, kuma su ne kawai suka yi nasarar yin rijista ta
hanyar NEXIT kafin a rufe ta.
Sannan kuma Ta kara da cewa daga cikin wadanda suka amfana 370,000 da suka yi nasarar yin rijista ta hanyar NEXIT Portal, wadanda suka ci gajiyar
shirin 230,000 ne kawai suka samu nasarar shiga horon rance NEXIT tare da bayyana samunsu na horar da rance NEXIT, ta hanyar amfani da USSD Code * 45665 #.
Dan haka a yanzu haka an saki shortlist na kowace jiha da kuma Ranar da za,a fara Training:
Shiga nan domin duba shortlist na Jiharka
Duba ShortList na Jiharka Anan
Duba Jerin wajen da Za’ayi Training na kowacr Jiha
ga bidiyon yadda zakuyi
Allah ya bada Sa’a