Yadda Zaka Bude Bank Account Batare Da Kayi Amfani Da Bvn Ba A Banking NFP Microfinance Bank
Zaka iya bude account bank a bankin NPF MICROFINANCE BANK batare da kana da bvn ba ko Kuma muce batare da kayi amfani da BVN din ka ba,
Wasun mu suna da bvn wasun mu Kuma Basu da bvn Kuma sun cika bashin Nirsal musamman ma Wanda suka cika Nyif, su kuma Nyif baza su turo maka da kudin Nan ba har sai ka mallaki account sannan zaka Sami wannan Rancen Kudin Wanda daga baya ma Nyif sun ware bank Uku ne kawai zasu biya mutane wannan Rance kudin bankunan sun hada da
BOABAB,
LAPO,
NPF MICROFINANCE BANK
To idan har kana son bude account batare da kayi amfani da BVN ba zaka dealing na wannan number a wayar zaka sa *5757# idan ya bude maka zaka Sami option guda biyu kamar haka,
1create account to bvn
2create account no bvn
Idan bada bvn zakayi amfani ba sai ka Danna 2 zasu baka damar cika full details naka tinda daga Kan sunan ka har zuwa Kan su shekarun haihuwar ka
Sannan zakaga komai suna baka misalin sa kafin ka cika
Da zarar ka kammala cika bayanan ka completed zakaji alert ba account number naka ya sauka
Zaka iya amfani da ita wajen transaction na rancen kudin bashin NYIF,
Daga baya Kuma zaka iya zuwa bank su maka Linking na account din naka da bvn naka
Fatan nasara