Uncategorized

Yadda Ake Chajin Wayar Android zuwa 100% a Kankanin Lokaci

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Chajin wayar Android abu ne da yazama sana’a mai gwabi a wajen wasu matasan kasar nan musamman idan akayi duba da yadda rashin cikakkiyar wutar lantarki ya zama ruwan dare a kasar.

Yadda akeyin Chajin na wayar Android cikin karamin lokaci abu ne mai matukar mahimmanci, hakan yasa Arewatalent ta bincika domin al’umma su sami Karin haske game da yadda akeyinsa.

Dafarko idan zaka sanya chajin wayar ka yana da kyau ka lura da abubuwa kamar haka:

Idan wayar ya rage saura 15% ko kuma kasa da haka to kafin sanya wayar a chaji ka kasheta baki daya.

Za’a iya sanya wayar a wani fanni da ake kira (Flight Mode), ma’anar wannan fannin zai tsayar da komai na wayar naka kama daga service Wi-fi da dukkan wani application da yake acikin wayar.

Wannan hanya da aka ambata itace lamba daya wato akashe wayar baki daya, domin mutane dayawa basu fahimce cewa a yayin da waya take akunne kuma an sanyata a chaji yana daukan lokaci mai tsawo kafin ta cika izuwa 100%, inda wasu zakaga suna ta sayen sabuwar Chareger domin samun Chajin da wuri kuma a zahirin gaske ba laifin charger bane.

Hakana masu amfani da rumbun ajiyar chaji (Power bank) suma irin wannan hanya da aka ambata a sama zasu bi saboda masu amfani da ma’ajiyar chajin suna tafe suna aiki da wayar dan haka ba lallai ne ta samu chaji 100% ba saboda wayar na chaji yana kuma tafiya sakamakon aikin da akeyi da ita.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!