Download

Yadda Zaka Maida Screen Din Wayarka Kore, Ja Ko Blue Ta Yadda Hasken Bazai Cutar Da Idanuwanka Ba

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Yadda Zaka Maida Screen Din Wayarka Kore, Ja Ko Blue Ta Yadda Hasken Bazai Cutar Da Idanuwanka Ba

Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Jimirin Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Albarka Hikimatv.

Kai Tsaye Kamar Kullum A Yauma Zamu Kawo Muku Darasi Ne Akan Yadda Zakuyi Amfani Da Wani Application Wanda Zaiyi Matukar Taimaka Maka Wurin Kare Lafiyar Idanuwanka.

Mun Riga Munsani Cewar Amfanin Da Mukeyi Da Wayar Hannu Ta Android Ya Zame Mana Jiki A Yanzu, Babu Wata Mafita Ko Sauki Face Saita Hanyar Amfani Da Wayar Android.

Sai Kuma Yakasance Amfanin Da Muke Da Ita Yake Tafe Da Abubuwa Guda Biyu, Wadannan Abubuwa Sun Hada Da Amfani Da Rashin Amfani.

Abu Na Farko Shine Amfanin Wayar Android, Wayar Android Tana Da Matukar Amfani Ga Rayuwarmu Tayau Da Gobe Wannan Ma Shine Dalilin Dayasa Muke Ta Kokari Wurin Ganin Mun Mallaki Wayar Android.

Sannan Sai Rashin Amfaninta, Rashin Amfanin Wayar Android Wadda Ayau Zamuyi Magana Akansa Shine Kashe Idanuwa.

Tayaya Wayar Android Take Kashe Idanuwan Dan Adam, Amsa, Hasken Dake Fitowa Daga Cikin Wayar Android Yana Da Matukar Hadari Ga Lafiyar Idanuwanmu.

Domin Shi Wannan Farin Hasken Yana Da Matukar Hadari, Misali Mu Koma Makaranta Ta Boko Kun Riga Da Kunsan Cewar Yawan Kallon Takarda Fara Yanasa Mutum Zubda Hawaye A Wasu Lokutan, To Haka Kallon Screen Din Waya Yake Da Wannan Illar Matukar Hasken Fari Ne.

Wannan Dalili Yasa Mukayi Kokarin Samo Muku Wani Application Wanda Zaiyi Matukar Taimaka Muku Wurin Kare Lafiyar Idanuwanku.

Shi Wannan Application Zai Baka Damar Sanja Hasken Screen Na Wayarka Izuwa Duk Wasu Kaloli Da Kake Bukata, Kama Daga Green, Red, White, Black, Pink Da Dai Sauransu.

Zamu Ajiye Muku Link Na Wannan Application Domin Kusamu Damar Saukar Dashi Akan Wayoyinku Na Android Cikin Wayarka.

Download Now

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!