Muhimmiyar Sanarwa Ga Wanda Suka Cika Tallafin Kudi Na RRR
Assalamu Alaikum barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.
Kamar de yadda kuka sani hukumar Nassco wato (National Social Safety-Nets Coordinating Office) wanda ake bada tallafin Kudi na RRR sun fitar da muhimmiyar sanarwa kamar haka:
Ma’aikatar agaji da jinkai ta kasa
Ta ja kunnen Yan nigeria da su guji fadawa hannun Yan damfara Dake nuna kansu a matsayin wakilan Ma’aikatar ta
Wanda zaka Sami wasu suna karban kudade wajen Al’umma suna cewa sunayin register tallafin covid-19 ne
Ma’aikatar tayi bayanin hakan ne a ranar litinin din Nan ganin wani shafi yayi rubutu Kan cewa zai iya bayar da tallafin kudin RRR inda har ya ajiye number wayar sa domin a Kira shi
Sunyi maganar sosai ganin irin wannan rubutun da suka gani
Hakan yasa Ma’aikatar ta fitar da Sanarwar Gaggawa ga Al’ummar kasar Domi su guji fadawa hannun Yan damfara
A cigaba da bayanin Ma’aikatar ne ta bayyana cewa ta kusan kammala shirye shiryen ta na biyan tallafin kudi na RRR Wanda zasu bayar da naira 30k akalla mutane sama da 2 millions ne suka amfana da wannan tallafin.