Idan Har Kana Mining na Pi Network ya Kamata Kasan Wannan
Assalamu Alaikum jama’ar wannan website namu na Albarka barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana lpy.
A yau zanyi magana akan Pi Network
Kamar de yadda kuka sani wannan kalmar ta Pi network kusan kowa yasanta a wannan zamanin kasancewar mutanenmu kaso 70% bisa 100% sunayinsa tare da burin zata fashe kowa yayi kudi.
Tun kusan 2019 de aka fara mining na Pi network, wanda mutane daya daga wancan lokacin zuwa yanzu sun tara Pi network masu yawa kuma suna jiran ta fashe.
Karanta: Yadda zaka tara Pi Network dayawa
Abun daya kamata masu mining ku sani anan shine a gaskiyar magana farashin da ake cewa Pi zai kai, mawuyacin abu ne yakai wannan farashin domin kuwa idan har ya kai wannan farashin to duk wanda yake dashi zai zama yafi kowa kudi a garinsu, sannan kuma kasar da sukafi yawan masu amfani dashi zata zama kasa mai kudi a duniya, Nigeria tana kan gaba wajen yawan masu amfani da Pi. Kenan idan ta fashe a yanda ake ta fada, nigeria zata zama ta daya a duniya a kasar da tafi ko ina arziki. Wanda hakan abune mai wuya muddin turawan amera suna nan bazasu bari hakan ya faru cikin sauki ba.
Dan haka duk masu mining ya kamara su dena zakewa akan darajar da ake yadawa akan cewa zai fito a hakan, kawai de idan kana mining kaci gaba dayi, tunda ba kudinka kasaba kawai ka jira har ta fashe din.
Banci Pi network karya bane, amma nace kar asa rai akan farashin da mutane suke ta bashi, kawai aje aci gaba da Mining Allah yayi jagora
Ga Yadda zaka tara Pi dayawa koda bakada mutane a karkashin ka.
Yadda zaka tara Pi dayawa
Allah ya taimaka Allah ya bada Sa’a