Loan & Support

Kafin kayi Mining Na Pi Network ya Kamata Kasan Wannan

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Jama’a Assalamu Alaikum barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.

A yau zanyi magana akan Pi Network

A Iya nawa bincike na gano cewar Pi network ba komi bace illa karya da yaudara (scarming)

Ba cewa nayi ku Daina Pi network ba Amma ku Daina yaudarar kawunanku da Kuma mabiyanku kawai saboda karya da aka sharara maku Gameda pi network

Da farko dai duk Mai hankali da sanin ya kamata ya sani cewar coin Mafi girmar daraja a duniya itace Bitcoin price nata a yau 25th Aug shine 9.15M naira approximately

Amma Kuma wai ana yaudarar mutane da cewar Pi guda 1 zai fito akan kudin Nigeria Naira millian 100 + wannan babbar yau Darace

A kwai manya manyan coin a duniya wasu ko naira 1 basu Kai ba a tsawon shekaru har zuwa yau Amma ana saa ran zasu iya zarce haka Nan gaba

A bisa kiyasin masana harkar coins na duniya a bincike na na gono cewar Pi network zata iya fitowa akan $0.00003193 in naira zai zama 0.13 naira kenan idan kanada guda 1000 kudinka zai kama naira gonna shaa uku 13 naira

A bincikenan masana na duniya ya nuna cewar Pi Nan gaba zaiyi daraja sosai domin yadda duniya ta dauki magana akanshi domin kuwa ana saa ran Nan da 5years ana saran Pi daya zai Kai doller 22$ duk guda 1

TSOKACINA GA YAN UWANA A HANKALCE SHINE

Kasancewar Nigeria itace kasa na farko a duniya a harkar ko wannan Yaa Isa ya Hana Pi network daraja a duniya domin kuwa kasar Nan ta Sami lambar yabo a duniya na kasancewar kasa na gaba gaba wajen damfara Wani kau linma ance Nigerian ce ta daya ku bincika a google zaku gani

Abu na biyu shine kowa yasani cewar turawa suka raini kasashen African Kuma yau gashi Afritace ta daya a harkar Pi network kenan idan tazo a yadda wasau suke maku karya arzikin duniya zai koma African Kenen?

A HANKALCE shin Kuna ganin Hakan zai yiwu kuwa ?

Ku Daina yaudarar mabiyanku da Kuma Wanda suka amintaa da ku don Allah, ku fada masu gaskiya da gaskiya Mai raayi yayi Wanda baida raaayi ya barshi ba sai Kun sokawa mutane hawan jini ba

Saa Rai ga abinci shine ke kawo yunwa
Abdul-Atom.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!