Loan & Support
Ga Wata Sabuwar Dama Daga Kamfanin MTN Nigeria
Advertisement
Join Our Whatsapp Group
Jama’a Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lpy.
A yau nazo muku da wata sabuwar dama daga kamfanin MTN Nigeria wannan wani sabon shiri ne da kamfanin MTN suka kirkiro mai suna mPulse Spelling Bee
MTN mPulse Spelling Bee Competition. Wannan wata gasa ce da ke da nufin taimakawa ɗalibai a Najeriya domin su inganta Harshen Ingilishi, ƙwarewar rubutu da kuma samun kyaututtuka masu ban sha’awa.
Akwai matakai Guda 3 a wannan gasar
- Matakin farko: za a yi shi ne a gidan yanar gizon MTN mPulse kuma yana buɗe wa duk ɗalibai masu shekaru 9 zuwa 15.
- Mataki na biyu: Za a gayyaci manyan 1000 daga zagaye na farko ta hanyar wasiku don zagaye na biyu na gasar da za a yi a gidan yanar gizon mPulse.
- Mataki na uku: Dalibai 20 na farko da suka sami maki mafi girma daga zagaye na biyu za su cancanci zuwa mataki na uku (Grand Finale). Za a aika gayyatar ta wasiƙa
Domin shiga wannan gasa saika danna link din da yake kasa
Shigo nan don Cikawa
Allah ya taimaka