Yadda Zakayi Katin Zabe Ta Cikin Wayar ka Cikin Sauki
Assalamu Alaikum barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.
Kamar de yadda kuka sani Hukumar zabe ta kasa wato INEC ta fitar da hanyar da zakuyi gyaran katin zabenku da kanku ta hanyar amfani da wayoyon ku.
Tun a shekarar 2021 de hukumar ta bude shafin nata domin bawa masu sha,awar yin sabon katin zabe kokuma gyara ko chanja mazaba, wanda tun a lokacin mutane dayawa sukayi ta kokarin yi, har aka kai ga wasu daga ciki sun mallaki nasu
Ga Abubuwan da zaka iyayi a yanzu haka:
- New Voter Registration
- Review
- Tranafers
- Information update
- Collect your pvc
- Lost or Damage pvc
New Voter Registration: Idan sabuwar register zakayi shine zaka shiga wannan idan ya bude anan ne zaka cika bayanan ka
Review: Shine Idan kun yi rajista kuma har yanzu ba ku sake nazarin bayananku ba ta hanyar samar da hoton ku akan layi akan wannan dandali,
Transfer: amfaninsa shine Idan kun yi rajista kuma kuna son canza wurin kada kuri’a zuwa wata rumbun zabe,
Information update: idan kun yi rajista kuma kuna son sabunta ko gyara bayanan da ke kan Katin Zaɓenku
Collect your pvc: Idan kun yi rajista a baya kuma ba ku sami katin Zaɓen ku ba
Lost or Damage pvc: Idan kun rasa katin zabenku ko kuma idan PVC ɗinku ta lalace kuma kuna son maye gurbinsa
Domin Yin Register Danna Link din da yake kasa
Shigo nan domin yin katin zabe
Allah ya bada Sa’a