Tutorials

Banbancin Dake Tsakanin Google Search Da Google Playstore.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Banbancin Dake Tsakanin Google Search Da Google Playstore.

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Tarin Albarka Wato Hikimatv.

A Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Irin Banbancin Dake Tsakanin Google Search Da Kuma Google Playstore.

Akwai Banbance Banbance Da Dama Dake Tsakanin Manhajar Playstore Da Kuma Google Search.

Amma Bari Mu Kara Da Google Search, domin shi google search shine babba ko itace babbar manhaja ko website.

Google Search.
Google Search dai Wani website ne ko alamace wanda zaka iya rubuta wani abu kayi searching kuma kasamu wannan abu a different website.

A Google Search ne kadai Zakayi Searching Na Komai Da Komai Kuma Kasamu Akasin Sauran Manhaja Wadda Zakayi Nemi Iya Abinda Akacema Kawai Shine Aciki Ko Shi Ake Dorawa.

Misali A Google Search Zaka Iya Bincike Akan Abinda Ya Shafi Ilimi, Applications, Videos, Musics, Dama Dukkan Wani Abu Da Kake Bukata Ko Kake Son Kasani.

To Kunga Kuwa Idan Kulayi La,akari Zakuga Shi Google Ya Hada Komai Da Komai Babu Wani Abu Wanda Ya Gagari Google Search, wannan Yasa Google Yazama Na Farko Wajen Bincike Ko Neman Wasu Abubuwa Da Kake Bukata.

Sai Dai Inda Akasamu Matsala Shine Ba Kowane Ya Iya Bincike A Google Ba Mafi Yawan Mutane Suna Bibiyar Manhajar Youtube Ko Playstore Ko Netflix Domin Dauko Film Ko Applications Wanda Dukkan ABubuwan Da Zaka Saukar Dasu A Wadancan Shafukan To Akwaisu A Google.

Kai Akwaima Abubuwan Da Zaka Samesu A Google Search Wanda Bazaka Samesu A Playstore Ko Netflix Ba.

Saboda Haka Yana Da Kyau Ka Kasance Mai Amfani Da Google Misali, Zaka Iya Neman Film A Netflix Amma Su Hanaka Download Amma Idan Ta Google Ne To Zaka Iya Saukar Dashi A Kan Wayarka.

A Darasi Na Gaba Zamuyi Bayani Akan Yadda Ake Download Ta Google Domin Kuwa Download A Google Abune Mai Wahala Koda Kana Da Ilimi Akan Abun Zaka Iya Shiga Wani Website Din Kaga Film Amma Ka Kasa Saukar Dashi To A Darasinmu Na Gaba Zamu Kawo Muku Yan Dabarun Da Akeyi Wurin Saukar Ko Download A irin Wadannan Website.

https://hikimatv.ginsau.com.ng/2022/07/30/yadda-zaka-dawo-da-duk-wani-application-daka-dauko-daga-cikin-playstore-zuwa-kan-wayarka-file-manager/
Shikuma Playstore Wata Manhaja Ce Wadda Da Zarar Ka Mallaki Gmail Account To Zaka Iya Amfani Da Ita.

Manhajar Google Playstore Tana Da Saukin Mu,amula Domin Kana Search Na Wani Abu Take Zaka Ganshi Matukar Wannan Application Bashi Da Wata Damuwa.

Manahajar Playstore Tana Bada Damane Na Downloading Din Application Kawai, Acikinta Ba,a Daukowa Wakoki Ba,a Daukowa Videos, Sannan Ba,a Bincike Akan Wani Abu Daya Danganci Ilimi.

Sannan Ita Wannan Manhaja Kana Iya Ganin Abinda Ka Daukone A Iya Cikin Wayarka Ne Wato Main Menu Na Wayarka Duk Application Din Daka Saukar Baya Hawa Kan Memory Ko Phone Din Wayarka, Zai Tsayane Kawai A Cikin Wayarka Wanda Daka Gogeshi To Sai Dai Ka Kara Saukar Da Wani.

Munyi Bayani A Baya Akan Hanyar Da Zaka Dawo Da Application Din Daka Saukar Daga Playstore Zuwa Kan Wayarka Zaka Iya Duba Wannan Posting Din Idan Baka Karantashiba A Baya.

Kinda Dukka Dukka Anan Muka Kawo Karshen Wannan Darasi Inda Muke Fatan Zaku Kasance Damu Domin Karanta Sabon Darasinmu Na Gaba Akan Yadda Zaka Koyi Download Na Komai A Google Kasancewar Akwai Abubuwan Da Bazaka Samesu Ba Face A Google.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!