Muhimmiyar Sanarwa Daga Hukumar Npower
Assalamu Alaikum jama’a Barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana lafiya.
Hukumar Npower sun fitar da muhimmiyar sanarwa ga dukkan wadanda suka cike aikin npower, wadanda sukayi nasarar samu dama wanda basuyi nasaraba.
Sanarwar itace: a kwanannan akan samu wasu bata gari wanda suke yawo a social media suna karban bayanai na wadanda suka cike aikin npower musamman wadanda aka fara biyansu, kunsan wasu daga cikin wadanda aka fara biyan nasu suna samun matsala wajen biyan nasu domin har yanzu wasu daga ciki suna samun tsaiko na rashin biyansu kudin nasu, hakanne yasa wasu bata gari suke amfani da wannan damar su biyo ka ta private suce maka zasu gyarama domin a biyaka kudinka.
Kokuma idan baka cikin wanda aka amince dashi suce daga hukumar npower suke zasuyi yadda za ayi domin a amimce dakai kokuma a turo maka kudinka. Zasu karbi bayananka kamar, Gmail, password, npower Id, da sauransu.
Dan haka hukumar npower suna kira ga mutane kan cewa wannan ba daga su bane kar wanda ya bayar da wani bayaninsa, yan damfara ne suke bi suna karba, dan Haka sai ayi kokari a kiyaye domin kuwa suna nan suna yawo a social media.
Allah ya kiyaye