Yadda Zaka Cike Sabon Tallafi Daga Youtube Black Voices
Jama’a Assalamu alaikum warahamatullah, Barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka HikimaTv.
A yau nazo muku da wani sabon tallafi da wata kungiya mai suna Youtube Black Voice.
Ita de wannan kungiya zata bada tallafin ne a bangarori kamar haka:
- Content Creator
- Artist
- SongWriter
- Producer
Content Creator: shine wanda ya mallaki channel wato yake da channel tasa ta kansa koda kuwa baida bai cika ka’idar da youtube suke bukataba inde yana da channel kuma yana kirkirar videos nasa yana dorawa to shine Content creator
Artist: Shine mai zane wato irin wanda suke kirkirar wasu zanen hotuna kokuma suyi zanen abubuwan amfani ko mutane sune artist.
SongWriter: Shine mutumin da yake rubuta waka shima zai iya cike wannan tallafin.
Producer: Shine mai shiryawa kamar shirya film ko wani abu wanda ya danganci bangaren nishadantar wa.
Wadannan sune wanda zasu iya neman wannan tallafin dan haka idan kana daya daga cikin wadannan abubuwa saika duba link dake kasa ka shiga domin cikawa
Shigo Nan
Allah ya bada sa’a