Loan & Support

Yadda Zaka duba ko kana Cikin Wanda Zasu Samu Tallafin Kudi na NG-Cares

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Jama’a Assalamu Alaikum Warahamatullah Barkanmu da sake kasancewa damu a wannan shafin namu mai Albarka na HikimaTv

Ng-Cares: Shiri ne da gwamnatin taraiyya ta fito dashi domin tallafawa matasa yan nigeria da kudi domin su dogara da kansu.

Idan baku mantawa wannan shiri na Ng cares ayi ta cike cikensa tun a kwanakin baya, wanda har mutane dayawa suka cike,

A yanzu haka de sun sake fito da sabo tsari domin dubawa ko kana daga cikin wanda zasuyi nasarar samun tallafin.

Yadda zaka gane ko kana cikin wanda zasu samu tallafin shine kamar haka:

Hanyoyi biyu ne, na farko suna tura sako ta message wanda yake dauke da wani Link wanda zaka shiga ka cike sauran bayananka, na biyun kuma shine wani link ake shiga domin a duba matsayin ko kayi nasara.

Yadda zaka duba ko zaka samu tallafin Ng care:

Da farko zaka shiga wannan Link din
https://ngcaresbusiness.org/

Idan ka shiga saika zabi jiharka sannan ka danna Go to portal

daga nan zai kaika shafi na gaba saika zabi bangaren abun daka cike a lokacin da kayi register a baya

Bayan ka zaba saika danna inda aka rubuta Get Vetted

Daka danna zai kawoka inda zaka rubuta number wayar ka, saika rubuta number ka wacce kayi Register na Ng cares da ita a baya.

Bayan ka rubuta saika danna Submit, shikkenan idan sun karbeka zakaga ya wuce dakai shafi na gaba inda zaka cike sauran bayananka da kuma bayanan bankin ka da kuma bayanan kasuwancin ka, bayan ka gama saika danna Submit shikkenan.

Amma wasu kuma ana tura musu message kai tsaye ta wayoyinsu don haka sai a sa ido ana dubawa.

Dukkan wanda kuma ya gwada hakan baiyiba to karya damu insha Allah shima zaiyi domin sunabin abunne step step.

Allah ya bada sa a

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!