Loan & Support

Sabbin Abubuwa Guda Biyar (5) da Whatsapp Suka Fito Dashi A 2022

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Jama’a Assalamu Alaikum Barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka na HikimaTv.

Whatsapp de dayane daga cikin abubuwan da akafi amfani dashi a wannan zamani da muke cikin musamman wajen yin chat, kasuwanci, da sauransu, hakanne yasa ya zama wanda maza da mata sukafi amfani dashi.

Kamar yadda aka sani a kowace shekara ana samun sabbin tsare tsare wanda ake chanjawa ko ake dadawa domin a ingantashi ta yadda za,abawa masu amfani dashi damar yin wasu abubuwan wanda abaya babu su.

A yanzu haka de a wannan shekarar ta 2022 whatsapp ya fitar da wasu sabin abubuwan domin dadadawa masu amfani dashi.

Ga Abubuwan kamar haka:

  • Kara adadin member na Group: Kamar de yadda aka sani whatsapp a baya yana da limit na adadin mutanen da za a iya zubawa a cikin group wanda idan baku mantaba 275 ne amma yanzu ya miyar dashi zuwa 500
  • Change Language: Kamar de yadda kuka sani whatsapp da iya yaren turanci ake amfani dashi, amma yanzu sun kara sanya wani yaren wato yaren Hausa dan haka zaka iya miyar dakai zuwa yaren hausa ga yadda zakayi: Yadda ake chanja Yare a whatsapp
  • Jin voice note a ko ina: Kamar yadda kuka sani a baya whatsapp idan kana sauraran voice recording, dole saide ka jira har sai ya kare sannan ka fito domin idan ka fito voice din da kakeji zai katse, amma yanzu kanajin voice zaka iya fitowa kaci gaba da chat dinka.
  • Disappearing message: Wannan ma wata sabuwar hanyace wacce whatsapp suka fito da ita, amfaninta shine zaka kunna ta idan ka kunna zaka seta lokacin da kakeso duk message daka aika saiya goge kansa bayan wannan lokacin daka seta masa ya cika, domin shiga wajen ka shiga Setting, ka shiga Account, ka shiga Privacy, sai kayi kasa anan zakaga wajen.
  • Undo whatsapp status: Shima wannan wani sabon tsari ne wanda whatsapp suka fito dashi, amfaninsa shine idan kayi status bayan ya gama hawa, nan take daga kasa zakaga inda aka rubuta undo status, daka danna zakaga status din bai hauba, a maimakon abaya idan kayi status daka sakeshi babu damar ka hanashi hawa, amma yanzu kana da zabi.

Ta yaya zaka samu duk wadannan sabbin tsarukan: Abubun babu wuya kawai ka shiga google playstore sai kayi Update na whatsapp din naka shikkenan ka gama.

Allah ya taimaka

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!