Loan & Support

Abinda Yakamata Duk Wanda Yacike Tallafin Kudi NG Cares Wato 30,000 Yasani Both Wanda Aka Biya Da Wanda Ba,a Biya Ba.

Abinda Yakamata Duk Wanda Yacike Tallafin Kudi NG Cares Wato 30,000 Yasani Both Wanda Aka Biya Da Wanda Ba,a Biya Ba.

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wani Sabon Post Na NG Cares.

Wato Kamar Yadda Mafi Yawanku Kuka Sani Tallafin Kudi Na NG Cares Da Ake Badawa Ko Ince Da Gwamnatin Nigeria Take Badawa Domin Rage Radadin Da Ake Ciki Na Kangin Talaucin Da Cutar Korona Tazamo Silla Sun Samu Isa Amma Ga Wasu Mutanen Ko Ince Ga Wadanda Suke Da Rabo.

Gwamnatin Nigeria Dai Tayi Alkwarin Raba Naira Dubu Biyar Biyar Ne A Lokacin Da Aka Fara Cike Wannan Tallafi.

Inda Kuma Daga Baya Ta Fara Raba Wannan Dubu Biyar Biyar Din, Amma Saidai Bakowane Yasamu Wannan Dubu Biyar Din Da Gwamnatin Tayi Alkwarin Rabawaba.

Bayan Dai Raba Wannan Dubu Biyar Biyar Da Gwamnatin Ta Nigeria Tayi,Mutane Da Dama Sun Tofa Albarkacin Bakunansu, Wasu Dai Sunyi Allah Wadai Da Wannan Rabo Da Akayi Kasancewar Su Basu Samu Wannan Tallafi Ba.

Inda Wasu Kuwa Suka Saduda Tare Da Zuba Idon Ganin Abinda Zai Faru A Nan Gaba Domin Sun San Allah Ne Maiyin Yadda Yaso.

To Bayan Wata Daya Ko Ince Biyu Kwatsam Sai Mutane Suka Fara Jin Saukar Naira Dubu Talatin Talatin Inda Wasu Kuma Suka Rika Kin Saukar Naira Dubu Ashirin Da Biyar Biyar.

Da Farko Dai Mutane Basu Fahimci Mike Faruwaba Kasancewar Kamfanin Daya Turo Wannan Dubu Biyar Biyar Bashine Yake Turo Wannan Dubu Talatin Talatin Dinba.

To Daga Bayane Gaskiya Ta Bayyana Cewar Wannan Tallafi Da Aka Cike Ne Na Dubu Biyar Biyar Suke Hadewa Na Tsawon Wata Shida Suke Bawa Mutane.

Sun Fara Tura Wannan Kudaden Ne Dab Da Shiga Watan Azumi Inda Mutane Sukayi Matukar Farin Ciki Sakamakon Halin Da Ake Ciki.

To Duk Da Dai Gwamnatin Tayi Kokari Domin Akalla Acikin Kashi Uku Na Wadanda Suka Cike Wannan Tallafi Kashi Biyu Sun Samu Wannan Tallafi.

To Wadanda Dai Basu Samu Wannan Tallafi Ba Sun Shiga Damuwa Matuka Sosai Saboda Rashin Samun Wannan Tallafi, Inda Daga Baya Dai Suka Zubawa Sarautar Allah Ido.

To Bayan Wata Daya Wato Bayan Watan Azumi Ya Wuce Sai Kuma Ake Yada Jita Jitar Cewa Wai Ashirin Da Biyar Ga Watan Aprilu Daya Gabata Za,aci Gaba Da Bada Wannan Tallafi.

Amma Bayan Wannan Watanma Ya Wuce Shiru Kakeji, To Maganar Gaskiya Ita Harka Ta Gwamnati Kuma Gwamnatin Ma Federal Ba,a Musu Karan Tsaye.

Domin Kuwa Koda Mpower Da Kake Gani Wanda Aiki Sukewa Gwamnati Kuma Ka,ida Ne A Biyasu A Kowane Wata, To Bakowane Watan Ake Biyansu Ba.

Saboda Haka Abinda Yakamata Ku Sani Shine Babu Wani Mutum Dazaice Wai Ranar Kaza Za,a Raba Kaza Ko Gwamnati Zata Bada Kaza.

Atakaice Dai Kuyi Kokari Kuci Gaba Da Addu,a Idan Da Rabonka Zaka Samu Idan Kuwa Babu To Sai Dai Kayi Hakuri.

To Dukka Dukka Anan Muka Kawo Muku Karshen Wannan Bayani, Saiku Kasance Da Wannan Site Namu Mai Suna Hikimatv.ginsau.com.ng Domin Samun Sababbin Shirye Shiryenmu Akowane Lokaci.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!