Loan & Support
Abubuwan da Hukumar JAMB ta hana dalibai su shiga dakin jarawaba da su
Advertisement
Join Our Whatsapp Group
Hukumar shirya jarabawar shiga jami’a a Najeriya, JAMB ta bayyana abubuwan da ba za a bari dalibai su shiga da su dakunan rubuta jarabawa ba.
JAMB ta wallafa jerin abubuwan ne a shafinta na intanet. Ta kuma ba masu shirin rubuta jarabawar shawara, tana cewa kar su kuskura su kai wadannan kayayakin kusa da dakin rubuta jarabawar.
“Duk wanda ya yi biris da wannan shawarar, ba za a bari ya rubuta jarabawarsa ba”, inji hukumar.
Hukumar ta JAMB ce ke shirya jarabawar da ke ba dalibai damar shiga jami’o’in kasar.
Ranar 6 ga watan Mayun nan zuwa ranar 16 ga watan za a gudanar da jarabawar a fadin kasar.
Ga jerin abubuwan da JAMB ta hana masu son rubuta jarabawa shiga dakunan jarabawar da su:
- Dukkan wani littafi ko kasida ko abin karatu da rubutu
- Kyamarori da naurorin nadar sauti da makurofo da earpiece na sauraron sauti
- Na’urar lissafi, wato kwakuleto da ire-irensu
- Gilasai masu kyamara da ake leken asiri da su
- Wayar salula ko ma dukkan na’urorin sadarwa na latironi
- Alkaluman rubutu
Allah ya taimaka
©BBC_Hausa