Loan & Support

Muhimmiyar Sanarwa Ga wanda Suka Taba Cike Tallafin Kudi Na RRR

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Assalamu Alaikum Warahamatullah, Barkanku da sake kasancewa damu a wannan shafin namu mai Albarka na HikimaTv.

Ga wata muhimmiyar Sanarwa ga wadanda Suka Cike Tallafin kudi na RRR, Kamar de yadda kuka sani wannan tallafi na RRR shiri ne da Gwomnatin Nigeria ta shirya shi domin taimakawa masu kananan karfi ta hanyar basu tallafin Naira 6000 har tsawon wata Shida, wanda aka hadeshi ya zama Ana bayar da Naira 30’000 maimakon 6k din na tsawon wata Shidan.

Mutane dayawa sun amfana da tallafin Naira 30’000 na RRR musamman wadanda suka fara cikewa a mataki na Farko, sune suka faracin gajiyar wannan shirin.

Bayan nan kuma anci gaba da bayar da dama ga wadanba basu cikeba a baya, yayin da mutane dayawa suka nemi shirin kuma Alhamdulillah, sunyi nasara domin wasu daga ciki har an basu kudinsu.

A kwanannan ma an sake bude wannan tallafi na RRR wanda shima mutane dayawa suka Cike, sannan kuma daga baya akazo aka karbi bayanansu wasu kuma ba’a karba ba har yanzu.

Muhimmiyar Sanarwar Anan Ita ce:

Duk wanda yasan ya cika wannan tallafi na RRR to ya sani cewa an fara bi unguwanni ana karban bayanan wadanda suka cike domin a turo musu kudinsu, Dan haka idan har kasan ka cike wannan tallafi to anabi unguwa unguwa ana karban bayanai dan haka saika zauna cikin shiri, wasu kuma suna kiran mutane a waya ne suna karban bayanan nasu, dan haka ya danganta da yadda tsarin na unguwar yake.

Sannan kuma wasu unguwannin ana sake kafe sunaye na mutanen da sukayi Reginster RRR amma kuma ba,a turo musu kudin suba duk da An karbi bayanansu, to irin wadannan suma anabi ana sake karban bayanan nasu domin wanda suka bayar na farko baiyiba shiyasa ba,a turo musuba, dan haka idan kaga sunanka kuma.Koda a baya ka bayar bayananka to karka damu ka sake bayarwa kamar yadda suka bukata.

Abubuwan da suke karba sune kamar haka:

  • Account Number
  • Bvn number
  • NIN Number
  • Phone number
  • Photo
  • Date of bith

Wadannan sune wasu daga cikin abubuwan da zasu karba a wajen ku.

Abun Lura: Ku sani cewa wannan tallafi na RRR basa taba karban Abun daya shafi ATM card dinka, kokuma a turo maka OTP ace ka bayar daga RRR duk wanda ya tambayeka bayanan ATM KO OTP to na RRR bane, dan haka sai a kula sosai Sabi da Ana samun bata gari suna Shiga Cikin Lamarin domin suyi amfani da wannan damar su damfari Mutane.

Allah ya kiyayemu

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!