Loan & Support

Sanarwa ta musamman daga Kamfanin MTN

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Assalamu Alaikum Barkanmu da wannan lokaci fatan kowa yana lafiya.

Kamfanin MTN Sun fitar da wata muhimmiyar sanarwa ga dukkan wanda suke amfani da layinsu na MTN

Kamar de yadda gwamnatin Nigeria ta umarci hukumar sadarwa dasu kule dukkan Layukan da ba a hada su da NIN number ba, Wanda hakan yayi sanadiyar Kulle layikan sama da 72Millions.

Hakanne yasa kamfanin na MTN ya futar da wata sanarwa kamar haka:

Kamar yadda Aka Umarci kowane kamfanin Layi su rufe layuka, kuma suka Rufe din, to hakan Ya sanya wasu gurbatattun mutane Sun fito da wani sabon Salo domin su yaudari mutane ta hanyar fitar da Link wanda suke yadashi a kafafen sada zumunta wanda suke cewa ka shiga Link din domin Ka hade Layinka da NIN number ka, kokuma ka bude layinka idan An Rufe maka shi.

Kamfanin MTN suna gargadin mutane akan wannan link din dan haka Muddin kaci karo da irin wannan karka shiga domin ba daga su bane.

MTN sun kara da cewa inde ba daya daga cikin wannan hanyoyin ka ganiba, to basu bane.

Hanyoyin Hade Layi da NIN number Na MTN Sune kamar haka:

  • Deal: *785#
  • Chat with Zigi on +234903300001
  • My MTN NG App
  • Text NIN to 785
  • Visit: www.mtn.Ng

Wadannan hanyoyi guda biyar sune kadai hanyoyin da zaka iya hade layinka na MTN da nin number ka, sabanin wadannan hanyoyi biyar kuma ba daga su bane, dan Haka sai a kula dakyau.

Sannan kuma suna sake shawartar mutane kan cewa idan baka gane wani abun ba, kawai kaje office na MTN mafi kusa dakai.

Allah ya bada Sa’a

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!