An Sake Bude Shafin P-Yes Domin Bada Tallafi Daga Gomnati
Jama’a Assalamu alaikum, Barkanmu da wannan lokaci sannun mu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka na HikimaTv
Kamar de yadda kukaji na fada an sake bude shafin bayar da tallafi daga gomnati na P-yes
Wannan Wani program ne mai suna P-yes wanda tun farkon mulkin shugaba buhari a 2016 aka fara gabatar dashi, wanda mutane sukayi ta nema a shekarar 2019.
Amma kuma daga wannan lokacin a 2019 ba,a sakejin labari game da shirin ba, to amma yanzu haka sun sake dawo da shirin kuma ana kyauta zaton a wannan karon za,a amfana da wannan shirin.
Hakanne ma yasa suka sake bada damar wanda sukayi Register a shekarun baya su sake Update na bayanansu, Sannan kuma suka sake bude sabuwar dama ga wanda basu tabayin Register ba.
Dan haka yanzu ga bayanin yanda tsarin yake a takaice:
Wannan wani shiri ne tare da Tsarin Karfafa Matasa na Shugaban Kasa, P-YES an tsara shi ne don gudanar da hadin gwiwa da gwamnatocin Jihohi, kungiyoyi masu zaman kansu da masu zaman kansu, don samar da wani tsari na saukaka ayyukan samar da ayyukan yi da karfafa matasa a Najeriya. Manufarmu ita ce karfafa matasan Najeriya ta hanyar samar da damammaki da kuma samar da yanayi na samar da arziki ta hanyar baiwa matasa sana’o’in hannu, ilimi da albarkatun da za su sa suyi amfani, ta yadda za a rage radadin talauci da samar da dimbin matasa masu karfin tattalin arziki wadanda suke da dabarun da za su iya amfani da su. ta hanyar kirkire-kirkire da ma’ana suna ba da gudummawa ga gina kasa
Dan haka yanzu sun sake bada damar sabunta bayanai ga wanda suka cike tallafin a baya, Sannan kuma sun sake bada damar yin sabuwar Register ga masu sha’awa.
Domin Sabunta bayananka shiga nan👇
Update old Application
Domin yin Sabuwar Register shiga nan👇
New Register Here
Allah ya taimaka Allah ya bada sa,a