Sanarwa ta Musamman Ga Wanda Suka Sake Neman Tallafin Kudi Na RRR
Barkanmu da wannan lokaci sannun mu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka na hikimtv
A yau magana ce akan wadanda suka nemi tallafin kudi na RRR
Kamar de yadda kuka sani wannan tallafi na RRR tallafi ne da gomnatin tarayya ta shirya shi wanda aka shirya bada tallafin naira 5000 na tsawon wata shida, wanda daga baya aka chanja tsarin ya zama naira 30’000 a maimakon 5000 da ake bayarwa na tsawon wata 6.
Tuni de wanda suka cke wannan tallafi tun a farko sune suka faracin gajiyar wannan shirin, yayin da a yanzu haka anaci gaba da biyan wanda suka nemi tallafin.
Dan Haka sanarwar itace a yanzu haka ana cigaba da sake karban bayanan wanda suka cike tallafin na kwanannan, dan haka idan kasan ka cike wannan tallafi kafin su rufe to saika zauna cikin shiri domin a kowane lokaci za,a iya zuwa a karbi bayananka kokuma a kiraka a waya kaje inda ake karban kokuma su bukaci ka tura musu.
Karanta: Yadda Zaka Gane ko kana cikin masu cin gajiyar Tallafin 30’000 na RRR
Note: Ammafa ku sani dole sai kun kula sosai domin ana samun bata gari suna amfani da wannan damar suna amsar bayanan mutane ta yanda zasu iya musu kutse a acc dinsu na banki su dauki kudi kokuma su ciyo maka bashi, dan Haka Sai a kula. Allah ya kiyaye mu ameen