Sanarwa ta Musamman Ga wanda Suka Cike Tallafin Kudi na Ng Cares
Barkanmu da wannan lokaci sannunmu da sake kasancewa da wannan shafin namu mai Albarka na hikimaTv
Kamar yadda kukaji na fada, wato sanarwa ta musamman ga wanda suka cike tallafin kudi na Ng cares.
Shide wannan tallafi na Ng cares tallafi ne da aka warewa kowace jiha dake fadin nigeria kimanin dallar amurna miliyan daya, domin a tallafawa matasa da kuma.Masu kananan karfi, da kuma wanda annobar korona ta shafa.
Hakanne yasa aka bude wannan tallafi kuma kowace jiha suka bada damar kowane dan jiya ya shigar da bayanansa, wanda tuni mutane sukayi ta shigar da bayanan nasu.
Sanarwa ta musamman din itace: Wannan tallafin na Ng cars duk wanda yasan ya nema to ya zauna cikin shiri, domin kuwa tuni wasu jihohin suka fara gabatar da shirib, dan Haka idan kasan ka cike to ka zauna cikin shiri, domin ana kyautata zaton a watan Afril za,a fara karban bayanan dukka wanda ya cika wannan tallafi.
Dan haka idan ka cika to ka zauna cikin shiri domin za,a karbi bayananka kamar haka:
- Bvn number
- Nin numbe
- Acc number
- Phone number
- Email Address
- Smedan certificate
Wadannan sune abubuwan da ake tunanin zasu karba a watan afrilu da ake sa ran za a gabar da shirin.
Dan haka saika tabbatar kana da wadancan abubuwan kafin lokacin karban bayanan yazo.
Idan Kuma Bakayi Register na NG cares ba, har yanzu kana da damae yi kafin a rufe, ka shiga Apply dake kasa domin cikawa:
Apply Here
Idan kuma baka da certificate na smedan, ka shiga link dake kasa domin ka mallaki naka certificate din:
Yadda Zakayi Certificate na Smedan
Allah ya bada sa’a