Yadda Zaka Zama Agent Na NG-CARES
Assalamu alaikum jama’a barkanmu da wannan lokaci sannunmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai albarka.
A yau zanyi magana akan yadda zaka zama agent na jiharku a tsarin ng-cares,
Kamar de yadda kuka sani wannan tsari na NG Cares shiri ne da gwamnati ta shiryashi domin tallafawa matasa da kuma masu kananan sana’oi.
Sannan wannan shirin an tsarashi ne ga kowace jiha aka ware mata dala miliyan 20 domin ta gabatar da shirin ga yan cikinta.
To hakanne yasa suka bada damar zaban wakilai wato agent wanda zasu gabatar da wannan shirin.
Idan kun lura zakuga wani link da yake ta yawo na Ng cares, wanda idan kuka shiga link din zakuga suna muku bayani ne akan yadda zaku zama agent na jiharku, eh hakane amma akwai dan gyara dan gane da hakan.
Link din shine na zama agent din, amma ba kowa zai iya zama agent din ba sai wanda suka zaba, sabo da haka idan nasu zabe kaba basa bukatar ka shiga link din ka cike, dan haka dole sai sun zabeka sannan zaka shiga ka cike.
Yadda suke zabar mutun ya zama agent shine: wadanda suka cike wannan tallafi a farko, acikinsu ne ake zabar wasu daga ciki sai a kirasu a waya kokuma a turo musu sakon su ziyarci shafin zama agent domin su cike form na zama agent din.
Saide wasu haka kawai suna shiga suna cikewa batare da sunsan sai wanda aka zaba ba, Dan haka kada aci gaba da cikawa muddin baka cikin wanda aka bawa damar cikawar, yin hakan kuma zai iya sanyawa suyi Rejecting dinka.
Domin cike form din zama Agent saika shiga nan
Apply here
ga yadda zakuyi cikin video
Allah ya bada sa’a