Uncategorized
Yadda Za’a Duba Ko Katin Kasa (National I.D) Ya Fito
Advertisement
Join Our Whatsapp Group
Idan har an yi rajistar samun katin kasa na dan wasu tsawon lokuta sannan ba’a san ranar da za’a karba katin ba, ko kuma an sha zuwa offishinsu tambayar ko ya matsayin wannan kati yake amma kuma haka zalika ba’a ji sabon labari ba, wata kila kuma an gaji da ziyartar offishinsu har an cire tsanmani. hukumar NIMC a yanzu ta samar da shafin duba matsayin katin ta yanar gizo wanda zai bada damar sanin cewa ko katin ya fito ko dai har yanzu da saura. Ga cikakkaiyar hanyoyin da mutum zai bi ya duba matsayin katin sa na kasa a yanar gizo.
- Abu na farko dai shine, mutum zai ziyarci shafin NIMC a yanar gizo a wannan addreshin: https://touch.nimc.gov.ng/
- Idan an shiga sai a danna mabullin ‘proceed button’ wadda ma’anar sa karasa zuwa gaba
- Daga nan sai mutum ya cika wurin ababen da ake bukata na sunayen sa, wanda akwai wurin cika suna na farko kafin sunan karshen wato sunan uba, sai kuma ya saka lambobi na katin kasa da aka ba shi (yana jikin katin da aka bayar).
- Da mutum ya cike wadannan abubuwa da ake bukata sai ya danna mabullin ‘check now button’. Bayan an danna sai a jira na dan wasu daki kai, yana gama dubawa za’a nuna ma mutum matsayin katin sa. Ya fito ko kuma dai yana hanyar fitowa.
Allah yasa ayi sa’a