YADDA ZAKA HADA VIDEO INVITITION DA WAYARKA CIKIN SAUKI
Da farko Mutum zaiyi Saukar da Application din da akeyi wannan aikin da shi
Ga Wanda suke son koya zasu Shiga wajen da aka rubuta download now domin saukar da application din
SHIGO NAN DOMIN SAUKAR DA APPLICATION DIN
Da zarar kayi Installing na Application din a kan wayar ka to sai ka Shiga cikin application din
a) Daga kasa zakaga wata alamar kore sai ka danna ka shiga.
b) Sai a rubuta Sunan da akeso yakasance akan File din, bayan an saka sunan sai a danna “Create movie”
C) Yana dauke da abubuwa dayawa kamar haka:
“Background” zaka shiga wajen da aka saka alamar 1 sai ka zabi wace irin kala kakeso backgroung na aikinka ya kasance.
“Text” Shine rubututtuka da zakayi.
Misali: Iyalan wane suna gayyatar daurin auren yayansu” haka idan zaka kara rubuwa wata jimlar zaka dawo ka taba Text ka sake rubuta wani abinda kake son rubutawa Haka zakayi tayi har ka kammala rubuta dukkan abinda kake son rubutawa.
“Stiker” Idan akwai wani hoto karami da kakeso kasaka a gefe guda zaka iya daukoshi ka saka.
Misali zakaga wasu suna Sanya hoton ango da amarya wasu Kuma na iya ango ko amarya suke sakawa
“Hand” Shine wajen da zaka zabi kalar hannun da kakeso yananyin rubutun bayan ka gama.
“Music” Shine wajen da zaka dauko waka daga cikin wakokin wayarka da zaka hada rubutunka.
Ma’ana wakar da zata kasance akan wannan video da ka hada
wannan waje yana da matukar mahimmanci. Shine wajen da kana kan aiki duk motsi kadan kataba wajen domin zai na maka play na yadda aikinka yake tafiya.
Idan kana kan hada video Invitition dinka ko wani uzuri yazo zaka tashi, to kana taba wannan wajen domin yana saving dinsa a matsayin ajiya, duk lokacin da ka dawo zaka samu aikinka a shafin farko na app din “a”.
Shine wajen da idan kagama aikinka zakayi saving dinsa akan wayanka.