News

Najeriya Ta Ja Kunnen Kamfanin Facebook

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Ministan watsa labarai da al’adu na Najeriya Alhaji Lai Mohammed ya buƙaci shafin Facebook da sauran shafukan sada zumunta da su daina barin ƴan ƙungiyar IPOB da ke fafutikar kafa ƙasar Biafra su rinƙa amfani da shafin wurin neman tayar da zaune tsaye ko kuma haɗa rikicin ƙabilanci.

Ministan ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Talata bayan wata tattaunawa da ya yi tare da wakilan kamfanin Facebook.

Lai Mohammed ya bayyana cewa tun da gwamnatin tarayya ta ayyana IPOB a matsayin ƴan ta’adda, Facebook ba shi da hurumin ba yan IPOB damar bayyana ra’ayinsu.

Ministan ya bayyana cewa duk da an dade ana ta ƙorafi ga Facebook kan ayyukan ƴan IPOB, amma kamfanin bai yi komai ba da zai dakatar da su.

Ya ce a yanzu gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da sa ido kan Facebok da sauran shafukan sada zumunta a ƴan kwanakin nan domin tabbatar da cewa sun bi ƙa’idoji.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!