Loan & SupportTutorialsUncategorized

Kamfanin Layukan Najeriya Yana shirin ƙara kudin yin Kira da Data da aika Saƙo

Advertisement Join Our Whatsapp Group

Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta Najeriya ta ce ta samu takarda daga ƙungiyar kamfanonin sadarwa na ƙasar na neman yin ƙarin kuɗin kiran waya da kuma datasakamakon tsadar gudanar da ayyukansu.

Rahotanni a Najeriya sun ce takardar da ƙungiyar ta gabatar na neman yin ƙarin kashi 40 cikin 100 na farashin kiran waya da aika saƙo.

Kamfanonin na son yin ƙarin ne na kira dgaa N6.4 zuwa N8.95, farashin aika saƙo kuma zai koma N5.61 maimakon N4.

Sai dai Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC ta ce za a iya samu

dalilai masu ma’ana don buƙatar tana mai cewa babu ƙarin kuɗin da za a yi ba tare da nazarin farashi ba domin ƙayyade yadda ya dace, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ruwaito.

Hauhawan farashi a Najeriya kusan ya shafi ko wane ɓangare, yayin da masu saye da sayarwa suka fi jin tasirinsa.

Taɓarɓarewar darajar naira ya ƙara haifar da tsadar kayayyakin, musamman a ƙasar da ta dogara da shigo da kayayyakin buƙatu na yau da kullum daga waje.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!